Bayan Arangama da Bashir Ahmad, Davido Ya Yi Shaguɓe ga Gwamnan APC

Bayan Arangama da Bashir Ahmad, Davido Ya Yi Shaguɓe ga Gwamnan APC

  • Mawaki David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya ci gaba da jawo maganganu yayin da ake shirin zaben Osun
  • Davido yavmayar wa Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, martani bayan ya soki Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, kan salon mulkinsa
  • Okpebholo ya yi ikirarin cewa Adeleke ya fi mayar da hankali kan rawa maimakon gudanar da harkokin gwamnati yayin gangamin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Mawakin Najeriya, David Adeleke ya mayar da martani ga kalaman Gwamnan Edo, Monday Okpebholo kan sukar gwamnan Osun.

Mawaki Davido wanda aka fi sani da Davido ya yi martani ne ga gwamnan kan kawunsa, Gwamnan Osun, Ademola Adeleke wanda ke neman wa'adi na biyu a zaɓen da za a yi.

Davido ya taba gwamnan APC
Fitaccen mawaki a Najeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido. Hoto: Davido.
Source: Instagram

Martanin ya biyo bayan kalaman Okpebholo da ya yi ranar Alhamis, 6 ga Agusta, yayin wani gangamin yakin neman zaben APC gabanin zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya shiga tsaka mai wuya kan rufe asusun gwamnati da umarnin Tinubu

Cacar baki ta kaure tsakaninsa da Bashir Ahmad

Wannan rigimar Davido da Gwamnan ya biyo bayan cacar baki da ya barke tsakanin mawakin da hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad.

Mawaki David Adeleke Davido da Bashir Ahmad sun yi musayar kalamai masu zafi a X bayan cece-kuce ana shirin zaben jihar Osun.

Mawakin da aka fi sani da Davido ya yi wa Bashir Ahmad gori kan kuri'u 16 da ya samu a zaben fitar da gwani na APC a Kano lokacin da ya ke neman dan majalisar tarayya bayan kammala gwamantin Muhammadu Buhari.

Davido ya mayar da martani, lamarin da ya jawo muhawara kan siyasa da nishadi yayin da ake tunkarar zaben gwamnan Osun na 2026 da muke ciki.

Davido na samun matsala da kowa kan kawunsa gwamna Adeleke
Bashir Ahmad da mawaki Davido da suka kaure da cacar baki. Hoto: Bashir Ahmad, Davido.
Source: Facebook

Martanin Davido ga Gwamna Okpebholo na Edo

Yayin da yake jawabi ga mahalarta gangamin, Gwamna Okpebholo ya bukaci masu kada kuri’a su cire Gwamna Adeleke daga mukaminsa, yana zargin cewa gwamnan ya fi mayar da hankali kan rawa maimakon gudanar da gwamnati, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Kuri'u 16 ka samu': Davido da Bashir Ahmad sun kaure da faɗa, sun ƙunyata juna

Da sanyin safiyar Juma’a, Davido ya mayar da martani ga sukar ta shafinsa na sada zumunta, inda ya yi tambaya kan tarihin karatun Gwamna Okpebholo na jihar Edo.

Mawakin ya wallafa hoton wani takardar sakamakon jarrabawar WAEC da ya ce na gwamnan ne, wanda ke nuna maki marasa kyau da dama, ciki har da D7 da E8.

Duka wannan arangama na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a Osun wanda kawunsa mai gwamna mai ci Ademola Adekeke ke neman wa'adi na biyu.

Rarara ya caccaki mawaki Davido

Mun ba ku labarin cewa babban mawakin da ke yi wa jam'iyyar APC waka, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana game da rashin tsaro da ya addabi tarayyar Najeriya.

Rarara ya magantu ne bayan fitaccen mawakin Najeriya da aka fi sani da Davido ya nuna sunayen daliban Oyo da aka sace a Amurka.

Dauda Kahutu ya nuna rashin jin dadi game da abin da Davido ya yi, yana cewa hakan zubar da mutuncin Najeriya ne a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.