Babbar Magana: An Gano Sababbin Hukumomi 2 da Aka Kafa ba Tare da Izinin Shugaba Tinubu ba
- Hukumar ICPC ta gano cewa Adeniyi Matthew Adeyemi ya kirkiri wasu hukumomin gwamnati biyu na bogi baya ga PFIPC
- Hakan na kunshe ne a cikin rahoton binciken da hukumar ICPC ga mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yau Alhamis, 6 ga Agusta, 2026
- ICPC ta ce za ta gurfanar da Adeyemi tare da binciken jami'an gwamnati da ake zargin sun taimaka masa wajen aikata wannan damfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gano wasu karin hukumomin gwamnati biyu na bogi da aka kirkira karkashin hukumar PFIPC.
ICPC ta zargi Adeniyi Matthew Adeyemi, wanda ya bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), ne ya kirkiri hukumomin biyu.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN), ne ya bayyana hakan a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan mika rahoton wucin gadi na binciken Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
ICPC ta miƙa wa Tinubu rahoton abubuwan da ta gano kan badakalar kafa hukumar bogi
Musa Aliyu ya ce binciken ya tabbatar da cewa Adeyemi bai taba samun nadin gwamnatin tarayya ba, sannan kuma bau wata doka da ta kafa PFIPC.
A cewarsa, takardar nadin da Adeyemi ya rika amfani da ita bogi ce, yayin da ya kuma kwace tsohon ofishin Presidential Economic Advisory Council (PEAC) tare da amfani da shi wajen gudanar da ayyukansa.
Ya ce hukumar ta bogi ta rika yin karya da sunan gwamnati, kwaikwayon hukumomin gwamnati da kuma gudanar da wasu ayyukan da suka saba wa doka, ta hanyar amfani da gibin da ke tsarin tantance bayanai da sa ido tsakanin hukumomi.
An gano karin hukumomin bogi biyu
Shugaban ICPC ya ce binciken ya gano karin hukumomin bogi guda biyu, wato FCT Investment Promotion Agency (PIFA) da kuma Foreign Investment Promotion Agency (PIPA)
A cewarsa, Adeyemi ya kirkiri wadannan hukumomi ne ta hanyar amfani da takardun dokoki na bogi, sannan ya bude asusun banki domin gudanar da ayyukan da ba su dace ba.
"An kirkiri wadannan hukumomi ne da takardun dokoki na bogi, sannan aka yi amfani da su wajen bude asusun banki domin gudanar da haramtattun ayyuka," in ji Aliyu.

Source: Twitter
Yadda aka sauya wa hukumar bogi suna
Ya kara da cewa Adeyemi ya sauya sunan hukumar daga Foreign Investment Promotion Council zuwa Foreign Intervention Promotion Council, tare da kokarin fadada aikinta har zuwa tara kudaden shiga.
Aliyu ya bayyana cewa binciken bai kammala ba, yana mai cewa ana ci gaba da tattara karin hujjoji domin gurfanar da Adeyemi da duk wadanda ake zargin sun hada baki da shi.
ICPC ta mika rahoton bincike ga Tinubu
Kun ji cewa hukumar ICPC ta mika wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu rahoton wucin gadi kan binciken PFIPC ta ake ta magana a kanta.
Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu.
Binciken ya nuna akwai gibin tsarin tantancewa da sa ido tsakanin hukumomin gwamnati, lamarin da Adeyemi ya yi anfani da shi saboda sakacin wasu jami'an gwamnati.
Asali: Legit.ng
