Gwamna Sule Ya Fadi Babban Abin da Yake So a Rika Tuna Shi Bayan Barin Mulki
- Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce burinsa shi ne a tuna da shi a matsayin wanda ya fitar da jihar daga mawuyacin hali
- Sule ya ce gwamnatinsa ta inganta hadin kan al’umma, rage tasirin jam’iyyun adawa, tare da kara bunkasa masana’antu
- Gwamnan ya bayyana Nasarawa a matsayin “lu’u-lu’u da ke boye”, yana mai cewa gwamnatinsa ta bude damarmakin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana babban abin da ya yi a jihar wanda yake son a rika tuna wa da shi.
Gwamnan ya ce yana son a tuna da shi a matsayin wanda ya sauya jihar tare da fitar da ita daga mawuyacin hali kafin wa’adinsa ya kare a watan Mayun 2027.

Source: Facebook
Sule ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya yi bayani kan nasarorin gwamnatinsa da irin abin da yake son bari a jihar.

Kara karanta wannan
2027: Babban jigon APC a Arewa ya tada rigima, ya ce ba zai sake tallata Tinubu ba
Kokarin da Gwamna Sule ya yi
Gwamnan ya bayyana Nasarawa a matsayin wani “lu’u-lu’u da ke boye” lokacin da ya karbi mulki, yana mai cewa gwamnatinsa ta yi kokarin gano damarmakin jihar da kuma kara fito da ita fili.
Ya ce yana son a tuna da shi saboda fitar da Nasarawa daga mawuyacin hali, yana mai cewa yanzu an “wanke lu’u-lu’un” kuma jama’a sun fara ganin kyawunsa a fili.
Ya ce:
“Ina son a tuna da ni a matsayin wanda ya fitar da jihar daga mawuyacin hali. Jihar lu’u-lu’u ce da ba a goge ba; yanzu mun wanke lu’u-lu’un, kuma jama’a za su iya ganin kyawunsa a fili.”
A cewarsa, gwamnatinsa ta kuma samu nasarar karfafa hadin kan al’ummar jihar tare da rage tasirin jam’iyyun adawa.

Source: Facebook
Gwamna Sule ya magantu kan rikicin siyasa
Gwamna Sule ya ce a halin yanzu, mafi yawan sabanin siyasa da ake samu a jihar na faruwa ne tsakanin ‘yan jam’iyyar APC mai mulki, ba tsakanin APC da jam’iyyun adawa ba.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin masu adawa a yanzu su ne mutanen da suke ganin an zalunce su ko kuma ba su ji dadin rashin nasarar da suka samu a zabuka ba.
Gwamnan ya kuma bayyana bunkasa masana’antu da inganta damar tattalin arzikin jihar a matsayin wasu daga cikin muhimman nasarorin da yake fatan gwamnatinsa za ta bar wa Nasarawa.
Ya ce jihar yanzu ta fi hadin kai, ta samu karin ci gaban masana’antu, sannan damarmakin tattalin arzikinta sun fara bayyana sosai.
Gwamna Sule ya kori kwamishinoni 6
An ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya sallami kwamishinoni shida a wani karamin sauyi da ya ce zai kara inganta aikin gwamnati kafin zaben 2027.
Gwamnan ya musanta jita-jitar rusa majalisar zartarwa gaba daya, yana mai cewa sauye-sauyen da aka yi na dabarun gudanar da mulki ne.
Sakataren gwamnatin Nasarawa ya ce za a sanar da sabbin kwamishinoni bayan kammala dukkan matakan da suka dace.
Asali: Legit.ng
