Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Kashe Babban Jami'in Soja a Najeriya

Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Kashe Babban Jami'in Soja a Najeriya

  • Wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe Kanal Abdussalam Ude na rundunar sojojin Najeriya a gidansa da ke Abuja
  • Matarsa da direbansa da jami’in tsaronsa sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin da 'yan bindigan suka kai
  • Rahotanni sun ce Kanal Ude na shirin samun karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar kafin ya riski ajalinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wasu 'yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude, wani jami’i mai aiki a rundunar sojojin Najeriya a Abuja.

'Yan bindigan sun kuma harbi matarsa a gidansu da ke yankin Kurudu na babban birnin tarayya, Abuja.

'Yan bindiga sun hallaka Kanal a Abuja
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, an kai wa Kanal Ude hari ne jim kadan bayan ya dawo gida a yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka babban soja a Abuja, an raunata matarsa da wasu

Direbansa da jami’in tsaronsa ma sun samu raunukan harbin bindiga yayin harin da 'yan bindigan suka kai.

An yi yunkurin sace Kanal Ude

Majiyar tsaro ta bayyana cewa maharan sun yi yunkurin yin garkuwa da Kanal Ude, amma sai suka fuskanci turjiya daga gare shi.

Wata majiya da ke da masaniya kan binciken farko ta ce:

“Ya yi musu turjiya. Bisa abin da masu bincike suka gano, suna son su tafi da shi ne, amma ya yi fito-na-fito da su. Abin takaici, ya rasa ransa saboda haka.”

Bayan sun kasa tafiya da shi, ana zargin maharan sun harbe Kanal Ude sau da dama kafin su tsere daga wurin.

An garzaya da matarsa da direbansa da jami’in tsaronsa asibiti domin yi musu magani sakamakon raunukan harbin bindiga da suka samu, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Kanal Ude na shirin samun karin girma

Kisan Kanal Ude ya girgiza jami’an rundunar sojojin Najeriya, musamman ganin cewa yana shirin samun karin girma zuwa mukamin Birgediya Janar.

Marigayin dan asalin jihar Enugu ne, kuma ya taba rike mukamai masu muhimmanci a bangaren tattara bayanan sirri da yaki da ta’addanci a rundunar sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta ana tsaka da garkuwa da mutane a hanyar Kano

Ya halarci wasu ayyukan yaki da ‘yan tada kayar baya a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Haka kuma, an tura shi wasu ayyuka na musamman a kasashen Chadi da Faransa, inda ya bayar da gudunmawa wajen hadin gwiwar tattara bayanan sirri da tsaro.

Abokan aikinsa sun bayyana Kanal Ude a matsayin jajirtaccen jami’in tattara bayanan sirri da ake matukar girmamawa.

Sun ce jajircewarsa wajen gudanar da aiki ta sa ya samu yabo da karramawa daga jami’an rundunar soji.

An fara farautar maharan

Hukumomin tsaro sun fara bincike kan harin tare da kaddamar da farautar wadanda suka aikata laifin.

Wannan kisa ya sake tayar da damuwa kan hare-haren da ake kai wa jami’an soji masu aiki da wadanda suka yi ritaya a Abuja.

Ana nuna damuwa musamman kan jami’an da suka taba rike mukamai masu muhimmanci a bangaren ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri.

'Yan bindiga sun kashe Kanal a Abuja
Taswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lamarin ya faru ne kusan shekaru biyu bayan wasu mahara dauke da makamai sun kashe Birgediya Janar Uwem Harold Udokwere mai ritaya a gidansa da ke yankin Lokogoma na Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga kusan 200 sanye da kayan sojoji sun yi ta'asa a jihar Sokoto

Rahotanni sun ce marigayi Udokwere ya rasa ransa ne yayin da yake kokarin kare iyalansa, yayin da maharan suka tsere da bindigarsa da wasu kayayyaki masu daraja.

Ana sa ran binne Kanal Ude a Masallacin Mambilla da ke Abuja bisa koyarwar addinin Musulunci.

'Yan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun hallaka akalla nutane 15 a wasu hare-hare da suka kai a jihar Benue.

'Yan bindigan ɗauke da makamai sun kai sabon harin kan kauyukan Ugboju da ke ƙaramar hukumar Otukpo a jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng