"Ba Tsere ba ne"; APC Ta Ragargaji Peter Obi kan Taba Shugaba Tinubu

"Ba Tsere ba ne"; APC Ta Ragargaji Peter Obi kan Taba Shugaba Tinubu

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta kare Shugaba Bola Tinubu bayan Peter Obi ya yi iƙirarin cewa shugaban kasar ya gaji da mulki
  • Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce Tinubu na aiki daga safe zuwa dare kuma yana ci gaba da gudanar da manyan ayyukan ci gaba
  • Ya ce ayyukan gwamnati a fannonin ilimi, hanyoyi, tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama sun nuna cewa gwamnatin Tinubu na kan aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da iƙirarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Peter Obi, cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaji da mulki.

APC ta yi martanin ne bayan Peter Obi ya bukaci shugaban kasar da ya hakura da neman tazarce domin ya gaji.

Kara karanta wannan

Kabiru Gaya: 'Abin da mu ka tattauna da shugaba Tinubu a Abuja'

APC ta kare Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana haka yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na tashar Channels TV a ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.

Yilwatda ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa Tinubu ya gaji, yana mai cewa shugaban ƙasar na aiki daga safe zuwa dare wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

APC ta yi wa Peter Obi martani

Shugaban APC ya yi watsi da ra'ayin Peter Obi cewa ya kamata Tinubu ya janye kafin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

"Bari na tambayi Peter Obi, wai Tinubu zai shiga wasan dambe ne ko tseren mita 400?
"Kana nufin shugaban ƙasa da yake aiki daga safe har zuwa dare ya gaji? Waɗannan su ne batutuwan da muke magana a kai."

- Nentawe Yilwatda

Yilwatda ya yabawa shirye-shiryen gwamnatin Tinubu

Yilwatda ya ce miliyoyin 'yan Najeriya da ke amfana da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu ba za su goyi bayan kiran a cire shugaban ƙasa daga mulki ba.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Oluremi ta fadi yadda Tinubu ya tallafa wa yan kasa da abinci

Ya yi nuni da shirin bayar da rancen karatu na NELFUND, yana mai cewa ɗalibai da iyalai da ke cin gajiyar shirin na yaba wa da gwamnatin.

"Kana nufin sama da ɗalibai miliyan ɗaya da iyaye mata da ke cin gajiyar NELFUND za su riƙa addu'ar shugaban ƙasa ya yi ritaya?"

- Farfesa Nentawe Yilwatda

APC ta lissafo ayyukan da gwamnati ke yi

Yilwatda ya kuma bayyana cewa manyan ayyukan gine-ginen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa sun nuna ƙudirinta na bunƙasa ƙasa.

Ya ambaci titin bakin teku daga Legas zuwa Kalaba da kuma gina sababbin tashoshin jiragen ruwa a Kalaba, Akwa Ibom, Fatakwal, Ondo da Legas a matsayin wasu daga cikin manyan ayyukan gwamnatin.

Shugaban APC ya kare Tinubu
Farfesa Nentawe Yilwatda na jawabi a wajen taro Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Har ila yau, ya ce ana ci gaba da zamanantar da filayen jiragen sama a sassa daban-daban na Najeriya.

"Kun ga yadda ake sabunta filayen jiragen sama ƙarƙashin Ministan Sufurin Jiragen Sama. Wannan da sauran ayyuka da dama, har da waɗanda ake yi a Arewacin Najeriya, shaida ce cewa gwamnati na mai da hankali kan samar da abubuwan more rayuwa."

- Farfesa Nentawe Yilwatda

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Tinubu ya amince da aikin N46bn a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 46 domin gyara tashar jirgin sama ta Malam Aminu Kano (MAKIA).

Mai girma Bola Tinubu ya amince da kudaden ne domin sake shimfiɗa da kuma sake gina titin saukar jiragen sama na biyu a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng