Dan Najeriya Ya Ga Samu Ya Ga Rashi, Ya Rasa Damar Samun Fiye da Naira Biliyan 2 saboda AI

Dan Najeriya Ya Ga Samu Ya Ga Rashi, Ya Rasa Damar Samun Fiye da Naira Biliyan 2 saboda AI

  • Marubucinl dan Najeriya, Jerry Falade ya rasa kwangilar buga littafi da ta haura Naira biliyan 2.7 bayan zargin amfani da AI
  • Hukumar da ke wakiltarsa ta janye littafinsa bayan ta ce ba za ta iya tabbatar da cewa ba a yi amfani da fasahar AI ba
  • Falade ya musanta zargin, yana mai cewa AI ya yi amfani da shi ne wajen bincike kawai ba wajen rubuta littafin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Marubucin littafi a Najeriya, Jerry Falade, ya rasa kwangilar buga littafi da ta haura Dala miliyan biyu (kimanin Naira biliyan 2.7) bisa zargin amfani da fasshar AI.

Rahoto ya nuna cewa marubucin ya rasa wadannana makudan kudi ne bayan bullar zargin cewa an yi amfani da fasahar AI wajen rubuta ko gyara littafinsa na farko mai suna Call Me, I’ll Hide the Body.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bayyana dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka tsunduma cikin talauci

Jerry Falade.
Marubucin Najeriya, Jerry Falade, wanda aka ruwaito ya rasa kwangilar buga littafi ta N2.7bn Hoto: Jerry Falade
Source: Instagram

Tribune Nigeria ta ce littafin, wanda aka shirya fitar da shi a 2028, ya ja hankalin manyan kamfanonin buga littattafai har aka samu gasa tsakanin kamfanoni 14 domin mallakar hakkinsa.

Kamfanin Macmillan U.S ta hannun Minotaur Books ya lashe damar buga littafin a Amurka cikin wata yarjejeniya ta littattafai biyu da aka ce ta haura Dala miliyan biyu, yayin da HarperCollins ta sayi hakkokin buga littafin a Birtaniya.

Hukumar marubucin ta janye littafin

Sai dai daga baya yarjejeniyar ta rushe bayan hukumar da ke wakiltar Falade, Europa Content, ta janye littafin, tana mai cewa ba za ta iya tabbatar da cewa ba a yi amfani da AI wajen ƙirƙirarsa ba.

A wata wasiƙa da ta aika wa masu buga littattafai, hukumar ta ce tun farko ta amince da bayanin Falade cewa ya rubuta tare da gyara littafin ba tare da amfani da AI ba.

Sai dai daga baya ta ce ba za ta iya tabbatar da yadda aka sauya littafin daga rubutun farko zuwa sigar ƙarshe ba.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

Falade ya musanta amfani da AI

Marc Gerald na Europa Content, wanda ya jagoranci sayar da hakkokin littafin a Amurka, ya ce wani edita ne ya fara nuna damuwa kan yiwuwar amfani da AI.

Sai dai Falade ya musanta amfani da AI wajen rubuta littafin.

Murubucin ya ce:

"Na yi amfani da AI ne wajen bincike kawai, ba wajen rubuta littafin ba."

A cewarsa, ya yi amfani da wata AI mai bude tushe (open-source) a na'urarsa domin bincike kan wasu bayanai, ciki har da sinadaran da za su iya narkar da gawar mutum domin labarin aikata laifi, da kuma tabbatar da kalmomin Turancin Amurka.

An kama dan Najeriya da laifi a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa alkalin kotun Amurka ya samu wani dan Najeriya da 'yan wasu kasashe da laifin damfara ta yanar gizo, inda suka wawure dala miliyan 215.

Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka damfara sun kai sama da mutane 1,000 a jihohi 47 na Amurka da kasashe 19 a fadin duniya.

Yayin zaman kotun da aka yi, alkalin ya bayyana cewa bayan sun wawure makudan kudi daga mutane da dama sun tura su wani asusun.banki

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262