'Mutumin da Za a Dorawa Alhaki idan Wani Abu Ya Samu El Rufai'
Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce gwamnatin APC na tsare Nasir El-Rufai saboda siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ya yi zargin ana hana tsohon gwamnan Kaduna shiga zaɓen 2027 domin raunana jam'iyyar ADC mai adawa
Bolaji Abdullahi ya ce idan wani abu ya samu El-Rufai, za a ɗora alhakin hakan kan Shugaba Bola Tinubu
FCT, Abuja – Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan ci gaba da tsare Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Bolaji Abdullahi ya ce za a ɗora alhakin duk wani abu da ya samu tsohon gwamnan na jihar Kaduna, kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Kakakin na jam'iyyar ADC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da tashar Symfoni tv.
An yi zarge-zarge kan tsare El-Rufai
Bolaji Abdullahi ya ce ci gaba da tsare El-Rufai ba shi da alaƙa da doka ko hukuncin laifi, illa siyasa kawai.
Tsohon ministan ya kuma yi zargin cewa ana ci gaba da tsare El-Rufai ne domin hana shi shiga zaɓen shekarar 2027, da nufin raunana jam'iyyar ADC.
"To, ba mu san abin da ya faru ba, amma abin da yake a bayyane shi ne wannan ba batun doka ba ne, ba batun laifi da hukunci ba ne, siyasa ce."
"A yau ba a tsare Malam Nasir El-Rufai saboda ya aikata wani laifi ba, domin idan haka ne, kotu ce za ta yanke hukunci ta ce yana da laifi ko ba shi da laifi."
"Amma ci gaba da tsare shi ba tare da iyaka ba yana nuna akwai wata manufa. Shi ya sa muka yi imanin cewa gwamnatin APC na son ci gaba da tsare Malam Nasir El-Rufai domin tabbatar da cewa bai shiga wannan zaɓe ba, kuma bai ƙarfafa adawa ba. Wannan ne ainihin shirinsu."
- Bolaji Abdullahi
Ya ce El-Rufai ya taimaki Tinubu
Bolaji Abdullahi ya kuma ce El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan Arewacin Najeriya domin marawa Bola Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
"Lokacin da wasu a Arewa suke cewa dole sai ɗan Arewa ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Malam Nasir El-Rufai ne ya jagoranci haɗa kan Arewa domin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu tare da wasu mutane."
"Na kuma ga bidiyo inda Shugaba Bola Tinubu da kansa yake roƙon Malam Nasir El-Rufai kada ya bar ƙasar nan, domin gwamnati za ta buƙace shi."
- Bolaji Abdullahi

Source: Twitter
"Tinubu zai ɗauki alhaki"
Abdullahi ya kuma yi iƙirarin cewa lafiyar El-Rufai na ci gaba da tabarbarewa.
"Zan sake maimaita wannan a nan. Allah Ya kiyaye, idan wani abu ya samu Malam Nasir El-Rufai, Shugaba Bola Tinubu ya sani cewa, ko da ba da nufinsa aka kai ga hakan ba, za a ɗora alhakin hakan a kansa, kuma sakamakon abin ba zai kasance mai sauƙin hasashe ba."
"Ko dai ya saki Malam El-Rufai beli ya bar shi ya fuskanci shari'a, ko kuma ya ci gaba da tsare shi har zuwa ƙarshen wa'adin mulkinsa."
"Idan muka karɓi mulki, za mu binciki abin da ya faru, sannan a ɗora wa kowa alhakin da ya dace da shi."
- Bolaji Abdullahi
An kai karar likitan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar ICPCta shigar da ƙarar likitan Nasir El-Rufai gaban Hukumar Kula da Ayyukan Likitoci da Masu Haƙora ta Najeriya (MDCN).
ICPC ta nemi a hukunta Farfesa Bello Abubakar bisa zargin ƙirƙirar rahoton lafiya da aka yi amfani da shi wajen neman belin tsohon gwamnan na jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng


