'Yan Bindiga Sun Farmaki bayan Allah a Benue, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Farmaki bayan Allah a Benue, an Samu Asarar Rayuka

  • Aƙalla mutum 15 sun mutu a hare-haren da aka kai wasu al'ummomin Ugboju da ke ƙaramar hukumar Otukpo
  • An gano gawarwaki 14 a ƙauyen Efeyi-Ugboju, yayin da aka kashe mutum ɗaya a Ipom-Ugboju a hare-haren na 'yan bindiga
  • Shugaban ƙaramar hukumar ya buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen aiwatar da dokar hana kiwo a fili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Makurdi, Benue – Aƙalla mutum 15 ne aka ruwaito sun mutu a safiyar ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026 a wani harin 'yan bindiga a jihar Benue.

'Yan bindigan ɗauke da makamai sun kai sabon harin kan kauyukan Ugboju da ke ƙaramar hukumar Otukpo a jihar Benue.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Benue
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin da aka kai ƙauyen Efeyi-Ugboju ya fara ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga Kaduna da dare, sun kashe rayuka 30 sun kona gidaje

Sun bayyana cewa an gano gawarwaki 14 zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto.

Sun kuma ce an kashe mutum ɗaya a ƙauyen Ipom-Ugboju tun da safiyar ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.

Ana ci gaba da gano gawarwaki

Mazauna yankin sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, domin har zuwa misalin ƙarfe 11:30 na safe ana ci gaba da gano gawarwaki.

Sun ƙara da cewa an garzaya da mutane da dama da suka samu raunuka daban-daban zuwa asibiti domin samun kulawa.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi.

"Harin ya fara ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe kuma ya ci gaba har bayan ƙarfe 9:00. An kashe mutum 14 a Efeyi-Ugboju, sannan waɗanda ake zargi makiyaya ne masu ɗauke da makamai sun kashe wani mutum a Ipom-Ugboju tun safiyar Litinin." In ji shi

Shugaban ƙaramar hukuma ya tabbatar da harin

Shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da aukuwar harin yayin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An gano hanyar da aka kafa ma'aikatar bogi ta PFIPC

Ya ce an gano gawarwaki 14 daga Efeyi-Ugboju, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Ogiri ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa an kai harin ba tare da wata tsokana ba, kuma manufarsa ita ce kashe rayukan mutane marasa laifi.

"Babu wata tsokana. Sun zo ne kawai domin zubar da jini da kashe mutanenmu. An gano gawarwaki 14, yayin da wasu da dama suka samu raunuka."
"Mutane na rayuwa cikin tsoro, kuma akwai fargaba sosai. Mazauna maƙwabtan al'ummomi ma sun fara tserewa domin neman mafaka." In ji shi
'Yan bindiga sun kashe mutane a Benue
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An nuna damuwa kan rashin tsaro

Shugaban ƙaramar hukumar ya nuna damuwa cewa duk da kasancewar jami'an tsaro, ciki har da sojoji, 'yan sanda, rundunar MOPOL da Agro-Rangers, hare-haren na ci gaba da faruwa.

"Ban sani ba ko jami'an tsaron da ke wurin ba su isa ba. Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki na musamman wajen tabbatar da aiwatar da dokar hana kiwo a fili, domin komai yana da alaƙa da wannan." In ji shi.

Kara karanta wannan

Najeriya ta saye sababbin jiragen yaki, za a zafafa yakar 'yan ta'adda

A nata ɓangaren, jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Benue (PPRO), DSP Udeme Edet, ta ce har zuwa lokacin ba ta samu cikakken bayani game da harin ba.

'Yan bindiga sun bukaci N200m

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindigan da suka sace alkalin babbar kotun jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya, sun nemi a ba su kudin fansa.

Yan bindigar sun nemi Naira miliyan 200 daga iyalan alkalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruku Hassan Bunza, domin su sake shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng