Abubuwa 7 da 'Yan Najeriya Za Su Kiyaye yayin Neman Aikin Gwamnatin Tarayya
- Hukumar FCC ta bayyana kurakurai bakwai da kan rage damar samun aikin gwamnati ga 'yan Najeriya
- Hukumar ta gargadi masu neman aiki da su guji biyan kuɗi ko amfani da hanyoyin da ba na hukuma ba
- Hakazalika ta bukaci 'yan Najeriya su tabbatar da sahihancin bayanan daukar aiki kafin su gabatar da takardunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana kurakurai bakwai da ta ce kan hana 'yan Najeriya samun damar shiga aikin gwamnati.
Gwamnatin ta bukaci masu neman aiki su bi hanyoyin daukar ma'aikata na hukuma kuma su guji fadawa hannun masu damfara.

Source: Twitter
An bayyana hakan ne a cikin wani sakon wayar da kan jama'a da hukumar FCC ta wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.
A cewar hukumar, masu neman aiki da dama kan rage yiwuwar samun nasara saboda rashin bin ka'idojin daukar ma'aikata, bayar da bayanan da ba su dace ba ko kuma dogaro da hanyoyin da ba na hukuma ba wajen samun sanarwar guraben aiki.
Kurakurai bakwai da FCC ta lissafo
Hukumar ta ce ga kurakuran da ya kamata masu neman aiki su guje masu:
- Neman aiki ta hanyoyin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba
- Biyan wani kuɗi domin a taimaka masu samun aikin gwamnati
- Yin watsi da sharuddan neman aikin
- Makara har wa'adin neman aiki ya ƙare
- Bayar da bayanan da ba su dace ba
- Rashin shiri bayan kammala neman aiki
- Daukar cewa duk wata sanarwar guraben aiki da aka wallafa ta gaskiya ce
Gargadi kan masu damfara
FCC ta gargadi masu neman aiki da kada su dogara da shafukan yanar gizo marasa sahihanci, sakonnin kafafen sada zumunta ko kuma saƙonnin da ake tura wa juna.
Hukumar ta ce masu damfara kan kirkiri shafukan bogi da sanarwar daukar ma'aikata ta karya domin yaudarar masu neman aiki.
Saboda haka, ta bukaci 'yan Najeriya su tabbatar da duk wata sanarwar daukar aiki ta hanyoyin gwamnati da aka amince da su kafin su tura takardunsu ko bayanansu na sirri.

Source: Facebook
Kada a biya kuɗi domin aiki
Hukumar ta kuma gargadi masu neman aiki da kada su bai wa duk wani mutum kuɗi saboda alkawarin samar musu da aikin gwamnati.
Sanarwar ta ce:
"Masu neman aiki su yi taka-tsantsan da duk wanda ke neman a biya shi kuɗi ko kuma ke ikirarin zai iya tabbatar musu da samun aiki. Haka kuma muna ƙarfafa su su kai rahoton duk wata alama ta damfara ga hukumomin da suka dace."
Gwamnatin Zamfara ta dauki ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta fara aikin ɗaukar sababbin malamai 3,050 domin koyarwa a makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandare na gwamnati.
Gwamnatin Zamfara za ta dauki ma'aikatan ne a wani yunƙuri na magance ƙarancin malamai da inganta harkar ilimi a jihar.
Asali: Legit.ng

