Netanyahu Zai Gana da Trump bayan Tsagaita Wuta, an Ji Abin da Za Su Tattauna

Netanyahu Zai Gana da Trump bayan Tsagaita Wuta, an Ji Abin da Za Su Tattauna

  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu zai gana da Shugaban Amurka, Donald Trump a ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026
  • Ganawar shugabannin kasashen biyu za ta fi mayar da hankali kan yakin Iran da kuma batutuwan tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Haka kuma shugabannin na Amurka da Israila za su tattauna kan Lebanon da halin da ake ciki a zirin Gaza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Washington, D.C. – Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu zai gana da Shugaban Amurka, Donald Trump a Fadar White House ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.

Ganawar ita ce karo na farko tun bayan sake fara yakin Iran, lamarin da ya janyo sabanin ra'ayi a fili tsakanin shugabannin biyu.

Trump zai gana da Netanyahu
Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoto kan ganawar shugabannin biyu a ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Duk da cewa dangantakar Trump da Netanyahu ta fuskanci matsin lamba a wasu lokuta cikin 'yan watannin nan, bangarorin biyu sun yi kokarin rage wannan takun-sakar.

Yakin Iran ne kan gaba

Ana sa ran yakin Iran zai mamaye tattaunawar shugabannin, wanda ya fara bayan hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila kan Iran a karshen watan Fabrairu.

A cewar Washington, gwamnatin Amurka na son bai wa tattaunawar diflomasiyya damar samar da mafita.

Isra'ila ba ta shiga sabon rikicin da ya barke tsakanin Amurka da Iran ba, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Afirilu ta rushe a farkon wannan wata.

Wannan ita ce ganawa ta takwas tsakanin Trump da Netanyahu tun bayan dawowar Trump kan mulki a bara, kuma ita ce ta farko da za su yi ido da ido tun bayan fara yakin.

Netanyahu ya bayyana manufar ziyarar

Kafin ya bar Isra'ila ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026 Netanyahu ya ce wannan tafiya tana da muhimmanci sosai.

"Babbar dama ce, amma kuma babban nauyi ne. Za mu tattauna dukkan batutuwan da ke gabanmu, musamman Iran. Burinmu shi ne tabbatar da tsaronmu tare da fadada da'irar zaman lafiya a yankin."

Kara karanta wannan

"Ina da hujja": Al Mustapha ya yi magana kan batun rasuwar Janar Abacha

Da isarsa Washington a ranar Litinin da yamma, ofishinsa ya bayyana cewa Netanyahu ya halarci wani zaman tunawa da marigayi Sanata Lindsey Graham.

Haka kuma ana sa ran zai halarci bikin tunawa da Graham a ranar Talata.

Dangantakar Trump da Netanyahu

Dangantakar shugabannin ta yi tsami sosai a watan Afirilu yayin tattaunawar tsagaita wuta da Iran, inda Trump ya yi kalamai masu zafi kan Netanyahu.

Daga baya kuma Trump ya bayyana Netanyahu a wata hira da cewa mutum ne "mai matukar wahalar mu'amala."

Sai dai Netanyahu ya ce wadannan sabani na dabarun siyasa ne kawai, yana mai jaddada cewa suna da manufa guda dangane da yakin.

Netanyahu zai gana da Donald Trump
Firaministan kasar Israila, Benjamin Netanyahu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Lebanon da Gaza za su shiga tattaunawa

Ana kuma sa ran shugabannin za su tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da Amurka ta dauki nauyin kullawa tsakanin Isra'ila da Lebanon a watan da ya gabata, duk da matsalolin da ake fuskanta wajen aiwatar da ita.

Baya ga haka, za su tattauna halin da ake ciki a Gaza, yayin da kokarin diflomasiyya na farfado da yankin Falasdinawa da yakin ya lalata ya tsaya cik.

Kara karanta wannan

Amurka ta gano hatsarin da Mojtaba Khamenei ke da shi fiye da mahaifinsa kan nukiliya

Kusan shekaru uku bayan barkewar yakin tsakanin Isra'ila da Hamas, halin jin kai a Gaza na ci gaba da tabarbarewa, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare kan mutanen da sojojinta ke zargin mayaka ne.

Donald Trump ya cika baki

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya yi wa ma'aikatan masana'antar motoci a jihar Michigan abin alheri fiye da yadda iyayensu suka yi masu.

Trump ya yi wannan ikirari ne yayin da yake jawabi a cibiyar gwajin motocin kamfanin GM da ke Milford, a jihar Michigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng