Tashoshin Samar da Lantarki Sun Tsaya Cak da Aiki, an Dauke Wuta a Fadin Kasar Ghana

Tashoshin Samar da Lantarki Sun Tsaya Cak da Aiki, an Dauke Wuta a Fadin Kasar Ghana

  • Babbar matsala ta lalata tushen samar da wutar lantarki na Ghana, lamarin da ya jefa Accra, Kumasi da yankunan arewa cikin duhu
  • Kamfanin GRIDCo ya ce injiniyoyinsa na aiki domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa ba tare da jefa lafiyar jama'a cikin hadari ba
  • Rashin wutar ya zo ne kwanaki bayan rasuwar Sulemana Abdul Samed, mutumin da ya fi kowa tsayi a Ghana, wanda ya rasu yana da shekara 33

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Ghana - Ghana ta shiga cikin babbar matsalar rashin wutar lantarki bayan wata matsala da ta afku a babban layin rarraba wutar kasar, lamarin da ya jefa babban birnin Accra, cibiyar kasuwanci ta Kumasi da yawancin yankunan arewa cikin duhu.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na gwamnatin Ghana ya bayyana cewa matsalar ta tilasta wa wasu manyan tashoshin samar da wutar lantarki dakatar da aiki tun da sanyin safiyar Laraba.

Kara karanta wannan

Likitan El Rufa'i ya rubuta zungureriyar takarda, ya yi bayani kan zargin ICPC

An dauke wutar lantarki a fadin kasar Ghana
An shiga duhu da aka dauke wutar lantarki a wasu sassan Ghana. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An fara gyaran lantarki a Ghana

Kamfanin Ghana Grid Company Limited (GRIDCo) ya tabbatar da cewa injiniyoyi da masu kula da tsarin lantarki suna aiki ba dare ba rana domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa, in ji rahoton BBC.

Kamfanin ya ce ana gudanar da cikakken binciken fasaha domin gano ainihin musabbabin matsalar, sai dai bai bayyana lokacin da za a kammala aikin gyaran ba.

Rashin wutar ya shafi gidaje, kasuwanni da muhimman cibiyoyi a yankuna da dama. Mutane da dama sun gamu da matsalar zuwa wuraren aikinsu saboda wayoyinsu sun mutu, wanda ya hana su biyan kudin mota ta hanyar lantarki ko kuma yin anfani da manhajojin kiran tasi kamar Uber.

Haka kuma, kananan 'yan kasuwa da masu gudanar da ayyukan intanet sun fuskanci matsaloli, yayin da manyan cibiyoyi kamar asibitoci suka ci gaba da aiki ta hanyar janareto.

Matsalar da ta dade tana damun Ghana

Kara karanta wannan

'Babu yan bindiga a Niger': Gwamnati ta gano yadda aka samu rashin tsaro

Ghana ta dade tana fama da matsalar rashin wutar lantarki, wadda ake kira "Dumsor" a harshen Akan, ma'ana "kunna da kashe".

Duk da cewa an samu ci gaba a shekarun baya, tsarin samar da wutar kasar na ci gaba da fuskantar matsaloli saboda tsofaffin tashoshin samar da wutar lantarki da rashin isasshen gyare-gyare.

Gwamnatin Ghana ta ce tana kan gyaran wutar lantarki da ta lalace
Turakun rarraba wutar lantarki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Mutum mafi tsayi a Ghana ya rasu

Wannan matsalar ta zo ne kwanaki bayan rasuwar Sulemana Abdul Samed, wanda aka fi sani da mutumin da ya fi kowa tsayi a Ghana.

Marigayin mai shekara 33 ya rasu a wani asibiti da ke Tamale bayan ciwon raunuka da suka bayyana a kafafunsa ya tsananta.

An bayyana cewa yana fama da cutar gigantism, kuma a shekarar 2022 BBC ta auna tsayinsa wanda ya kai kafa bakwai da inci hudu.

Iyalan marigayin sun ce mutane da dama na ci gaba da zuwa gidansu domin jajanta musu tare da bayyana alhininsu kan rasuwarsa.

Shugaban Ghana ya ba mutane mamaki

A wani labari, mun ruwaito cewa, sabon shugaban Ghana, John Mahama, ya yi kuskuren kiran shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a matsayin shugaban Ghana yayin rantsarwarsa.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An hango yadda malaman makaranta masu yawa za su ajiye aiki a Borno

Yayin jawabinsa a wajen taron, Bola Tinubu ya tabbatar wa Mahama cewa Najeriya za ta ci gaba da bayar da gudunmawa domin ci gaban Ghana.

Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya yaba da hadin kai da ci gaban dimokuradiyya da ake samu a kasashen Afirka, musamman a Yammacin nahiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com