Manyan Labarai A Yau
’Yan ta’addan dauke da makamai da ake zargin na Boko Haram ne sun kai hari Bitirhuya a Adamawa, inda suka kashe mutane huɗu tare da ƙona gidaje da dama
Oba na Legas, Rilwan Akiolu, ya bayyana goyon bayansa ga wa’adin mulkin Tinubu na biyu, yana cewa babu gurbin shugaban ƙasa a Aso Rock na shekaru huɗu ko biyar.
Daliban manyan makarantun gaba da sakandare a jihohin Arewacin Najeriya sun amince da tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027.
Ƙungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Najeriya (MURIC), reshen jihar Sokoto, ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa.
Bincike ya gano cewa Peter Obi bai janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 ba, duk da halartar taron yaƙin neman zaɓen Gwamna Seyi Makinde a Abuja.
Sarkin Musulmi, mai alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci ’yan Najeriya su tantance alkawuran ’yan siyasa da kyau kafin kada ƙuri’a a zaɓen 2027.
Aliko Dangote ya ce ba ya son a ƙara kiran sa attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, yana son a san shi a matsayin wanda ke samar da arziki ga wasu.
Matatar Dangote ta bullo da hanyar da duk wanda ya sayi hannun jarinta guda 10 zai iya samun karin guda daya kyauta idan ya cika sharadin da ta gindaya.
Aƙalla fasinjoji tara ne aka kashe bayan wasu ‘yan bindiga sun buɗe wa wata motar haya wuta a mahadar tituna ta Dungus Junction da ke ƙauyen Kuru a jihar Filato.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari