BUK: Mace 'Yar Jihar Kano Ta Yi Zarra, Ta Samu Mukami a Majalisar Dinkin Duniya

BUK: Mace 'Yar Jihar Kano Ta Yi Zarra, Ta Samu Mukami a Majalisar Dinkin Duniya

  • Majalisar Dinkin Duniya ta nada Farfesa Rabia Sa’id ta Jami’ar Bayero da ke jihar Kano a kwamitin masana 21 kan yakin nukiliya
  • Rahoton da kwamitin zai mika nan gaba, zai taimaka wajen tsara manufofin rage barazanar nukiliya a shekarar 2027
  • Farfesa Rabia na daga cikin fitattun masana kimiyya da suka karya shingen jinsi a fannin STEM a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Majalisar Dinkin Duniya ta nada Farfesa Rabia Sa’id daga Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) cikin kwamitin masana kimiyya 21 da zai yi nazari kan illolin yakin nukiliya da kuma tasirinsa ga al’umma.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sashen yada labarai na jami'ar BUK ya fitar, inda ta ce nadin da aka yi wa Farfesa Rabia ya samo asali ne daga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 79/238.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya ƙaddamar da aikin da ba a taɓa ganin irinsa ba a Arewacin Najeriya

Rabia Said.
Farfesa Rabia Sa’id ta jami'ar BUK da ke jihar Kano a ofishinta Hoto: Rabia Sa'id
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa majalisar dinkin duniya ta kafa kwamitin nd domin domin duba manyan barazanar nukiliya da ke iya shafar rayuwar bil’adama.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa a shekarar 2027 domin taimakawa wajen tsara manufofin kasa da kasa kan rage hadarin nukiliya, tsaron duniya da kare rayukan jama’a.

Tarihin Farfesa Rabia Sa’id

Farfesa Rabia Sa’id, wadda aka haifa a Wangara da ke Jihar Kano, ta samu digirinta na farko (B.Sc), digiri na biyu (M.Sc) da kuma digirin digirgir (PhD) a fannin Kimiyyar Lissafi (Physics) daga Jami’ar Bayero Kano.

Daga baya ta samu tallafin karatu na Ford Foundation Fellowship inda ta kara samun digiri na biyu a fannin Muhalli da Ci Gaba daga Jami’ar Reading da ke Burtaniya.

Ta karya shingen jinsi a fannin kimiyya

Farfesa Rabia na daga cikin mata biyu na farko da aka nada a matsayin malamai a Sashen Physics na Jami’ar Bayero Kano.

Kara karanta wannan

Layi ya zo kan talakawa, gwamna zai raba Naira biliyan 4 a mazabun jiharsa

Nadinta ya taimaka wajen bude hanya ga mata matasa a Najeriya da ke son shiga fannonin kimiyya, fasaha, injiniyanci da lissafi (STEM).

Gudummawarta a fannin kimiyya

Baya ga gudummawarta a fannonin kimiyyar yanayi, sararin samaniya, lantarki da kimiyyar kwayoyin halitta, Farfesa Rabia ta shahara wajen amfani da ilimin kimiyya wajen magance matsalolin muhalli na zahiri.

Daga cikin nasarorin da ta samu akwai kirkirar makamashin briquette mai kare muhalli daga tarkacen aikin kafinta, wanda ya taimaka wajen rage dogaro da itacen girki a yankunan karkara da kuma dakile sare itatuwa.

Farfesa Rabia Sa'id
Farfesa Rabia Sa'id ta jami'ar BUK da aka nada a kwamitin Majalisar dinkin duniya Hoto: Rabia Sa'id
Source: Facebook

Nadin nata a kwamitin Majalisar Dinkin Duniya ya kara nuna irin gudummawar da Najeriya za ta iya bayarwa a fannin kimiyya da kuma harkokin diflomasiyya da tsaron duniya.

APRC ta yi maganar shugabancin UN

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar APRC ta ba Shugaban kasa, Bola Tinubu shawara game da shugabancin Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Shugaban APRC, Farfesa Edward Agbai ya bukaci Tinubu ya tsayar da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar Najeriya na mukamin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Agbai ya bayyana cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na buƙatar jagora mai gogewar shugabanci, tarihin kare dimokuraɗiyya da kuma ƙwarewar magance manyan ƙalubalen duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262