An Kori Manyan Jami'an Isra'ila saboda Gaza Cin Iran da Yaki
- Shugaban hukumar leken asiri ta Isra'ila (Mossad), Roman Gofman, ya tsige manyan jami'an hukumar guda biyu wadanda suka kasance a gaba wajen tsara shirin hambarar da gwamnatin Iran
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an guda biyu sune suka tsara shirin amfani da 'yan tsagerun Kurdawa da kuma ruruta zanga-zanga domin kayar da tsarin mulkin Musulunci na Iran
- Wannan mataki na sallamar jami'an ya zo ne sakamakon sabani da aka samu a tsakaninsu da shugaban hukumar, ko da yake ana sa ran za a sake ba su wadansu mukaman a cikin hukumar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tel Aviv – Shugaban hukumar leken asiri ta Mossad ta kasar Isra'ila, Roman Gofman, ya dauki matakin sallamar manyan jami'an hukumar guda biyu daga mukamansu biyo bayan faduwar shirin hambarar da gwamnatin Iran.
Rahoto ya nuna cewa daya daga cikin jami'an ya kasance shugaban bangaren leken asiri na Mossad tun watan Disamba, yayin da daya kuma yake jagorancin sashen da ke kula da al'amuran kasar Iran.

Source: Getty Images
Times of Israel ta bayyana cewa jami'an biyu na daga cikin wadanda suka tsara shirin gudanar da aikin soji domin rusa Jamhuriyar Musulunci ta hanyar amfani da kabilun marasa rinjaye na Iran da kuma ruruta zanga-zangar gama-gari
Yadda aka tsara kai hari Iran
An ruwaito cewa Firaminista Benjamin Netanyahu ya tattauna wannan shiri tare da Shugaban Amurka Donald Trump a watan Fabrairu domin lallashinsa su kaddamar da yaki kan kasar Iran.
Majiyoyin tsaro da tashar ta ambato sun ce jami'an biyu da Gofman sun fuskanci sabani tun farko, amma suka jaddada cewa tafiyarsu tana wakana ne bisa yarjejeniyar juna a matsayin wani bangare na sake tsara tsarin hukumar Mossad.
A cewar kafar labarai ta Anadolu, shirin na Mossad ya kunshi kaddamar da hare-haren sojin Isra'ila kan dakarun tsaron juyin juya hali na Iran (IRGC) a kan iyakar Iran da Iraki domin bude wa 'yan tsagerun Kurdawa hanyar shiga cikin kasar.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a

Source: Getty Images
Yadda aka tsara sauya mulkin
An ce Mossad ta tsara cewa dubban matasan Kurdawa ne za su shiga gaba wajen yaki har su kai ga birnin Tehran, wanda hakan ke da nufin karfafa gwiwar miliyoyin masu zanga-zanga don kayar da gwamnatin.
Har ila yau, shirin ya hango nada tsohon shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad, a matsayin sabon shugaban kasar.
Sai dai fitar labarin a kafafen yada labarai, matsin lamba daga kasar Turkiyya, da kuma fargaba daga bangaren Kurdawa sun sanya Washington janye hannunta daga shirin.
Maganar makaman Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nuna bacin ransa matuka kan rahotannin da ke cewa samfurin makaman sojin Amurka na zamani ya ragu sosai yayin yakinta da kasar Iran.
Trump ya yi amanna cewa fitar irin wadannan bayanan na iya raunana matsayin Amurka a muhimmin lokacin tattaunawa da Iran, yayin da yake ci gaba da barazanar amfani da karfin soji domin tilasta wa Tehran amincewa da yarjejeniya.
Kafafen labaran sun bayyana cewa wannan batu ya mamaye taron majalisar ministoci da aka yi a Camp David, inda Trump ya fusata kan yadda bayanan sirri game da makaman Amurka suka fita ga jama'a.
Asali: Legit.ng
