Yadda ake Shirin ba Kuri'a Kariya a Zaben Jihar Osun, An Tura Jami'an ICPC

Yadda ake Shirin ba Kuri'a Kariya a Zaben Jihar Osun, An Tura Jami'an ICPC

  • ICPC ta ce za ta tura jami'anta zuwa dukkan ƙananan hukumomi 30 na Jihar Osun domin sa ido kan zaɓen gwamna da za a yi ranar 15 ga Agusta, 2026
  • Matakin ya na daga cikin riga-kafi da ake yi na sayar da kuri'a ko aikata wani abu da zai jawo matsala a zaben da za a gudanar a cikin makonni
  • Hukumar ta yi gargaɗin cewa mai ba da kuɗi da mai karɓa wajen sayen ƙuri'a duk sun karya doka kuma za a kama su tare da gurfanar da su a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta sanar da cewa za ta tura jami'anta zuwa dukkan ƙananan hukumomi 30 na Jihar Osun.

Kara karanta wannan

Mabiyan Kwankwaso sun ɓullo da wasu dabaru da ka iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027

Ya bayyana cewa an yi hakan ne domin sa ido kan zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta, da nufin hana saye da sayar da ƙuri'a.

Za a tura jamia'a don hana cinikin kuri'a a Osun
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun Hoto: Ademola Adeleke
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwamishinan ICPC mai kula da Jihar Osun, Yusuf Olatunji, ne ya bayyana hakan yayin wata gangamin wayar da kan jama'a da hukumar ta shirya a Osogbo ranar Alhamis 7 ga watan Agusta, 2026 domin yaƙi da cinikin ƙuri'a.

Ana shirin tukarar zaben Osun

Daily Post ta ruwaito ICPC ta ce gangamin ya samu halartar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), ma'aikatan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da jami'an ICPC tare da wasu jami'an.

An fara gangamin ne daga Kasuwar Igbona, kafin a bi ta Old Garage zuwa yankin Olaiya, sannan aka kammala a Kasuwar Alekuwodo da ke Osogbo.

Da yake zantawa da manema labarai bayan gangamin, Olatunji ya ce manufar shirin ita ce isar da saƙon hukumar cewa cinikin ƙuri'a laifi ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya.

An shawarci masu zabe a jihar Osun
Wasu daga cikin katinan zaben yan Najeriya Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya ce:

"Mun fito ne domin sanar da al'ummar jihar cewa saye da sayar da ƙuri'a laifi ne a ƙarƙashin dokar Najeriya. ICPC ba za ta lamunci saye ko sayar da ƙuri'a ba, kuma duk wanda aka samu da laifi za a kama shi tare da gurfanar da shi."

Kara karanta wannan

Baya ta haihu: Kotu ta umarci INEC ta sauya sunan dan takarar APC cikin sa'o'i 48

Ya ƙara da cewa:

"Hukumar ta kammala shirye-shiryen tura jami'anta zuwa dukkan ƙananan hukumomi 30 domin sa ido kan zaɓen tare da tabbatar da an kawar da cinikin ƙuri'a."

An shawarci mutanen Osun kan zaben gwamnan

Ya buƙaci al'ummar Osun su kare mutuncin tsarin zaɓe ta hanyar ƙin amincewa da duk wani nau'in cin hanci a lokacin zaɓe.

A cewarsa:

"Kada ku bari wani ya yaudare ku da kuɗi. Duk wanda ya shiga wannan aiki, mai bayarwa da mai karɓa, doka za ta hukunta shi."

Olatunji ya ce saye da sayar da ƙuri'a na iya ba mutum kuɗi na ɗan lokaci, amma yana jawo mummunan tasiri ga dimokuraɗiyya na dogon lokaci.

Tinubu ya yi magana kan Osun

A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar EFCC ta koma kotu domin janye umarnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun bayan lamarin ya jawo maganganu da cece-kuce a kasar.

Kara karanta wannan

Dalilan EFCC na garkame asusun gwamnatin Osun kafin zabe

Shugaba Tinubu ya ce lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba saboda zaɓen gwamnan Osun ya rage saura kwanaki kaɗan, ganin cewar hakan ba shi da alaka da maganar siyasa ko zaben da za a gudanar.

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta 'yancin hukumomin bincike su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma baki ba duk da cewa ya tsoma bakin a cikin wannan al'amari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng