An Kashe Manyan Kwamandoji da Mayakan ISWAP da Boko Haram Suka Gwabza Fada

An Kashe Manyan Kwamandoji da Mayakan ISWAP da Boko Haram Suka Gwabza Fada

  • ISWAP ta kai wani hari na ba-zata kan mayaƙan JAS a yankin Bula Murge da ke ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa an kashe wasu manyan kwamandojin JAS yayin artabun da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu
  • Masu tsaro sun yi kira ga dakaru su yi amfani da wannan dama wajen ƙara matsa wa ƙungiyoyin lamba a dajin Sambisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Bama, Borno - Wani sabon mummunan rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin Boko Haram masu gaba da juna a jihar Borno.

Fadan ya barke ne bayan mayaƙan Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun kai wani harin kwanton bauna kan mayaƙan Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad (JAS).

'Yan Boko Haram sun yi da 'yan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Cikin gwamnoni 18 ya duri ruwa da EFCC ta fara bincike kan zargin karkatar da kudade

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yankin Gargash da ke kusa da Bula Murge, kimanin kilomita 11 Arewacin Miyanti da kuma kilomita 26 arewa maso gabashin garin Bama.

Rahotannin sun ce mayaƙan ISWAP sun kai harin ba-zata kan mayaƙan JAS, lamarin da ya jawo asarar rayuka masu yawa bayan an gwabza faɗa mai zafi.

An kashe manyan kwamandojin JAS

Daga cikin waɗanda ake zargin sun mutu akwai wasu fitattun kwamandojin JAS da aka bayyana sunayensu da Abu Ubaida, Modu Kori, Alhaji Modu, Mure, Zarkawi, Sheriff da Modu Maye.

Majiyoyin sun ce waɗannan mutane suna taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar a yankin.

An kuma bayyana cewa harin ya jefa mayaƙan JAS da suka tsira cikin ruɗani, yayin da bayanan sirri da aka samu suka nuna cewa ƙungiyar ta fara shirin kwashe mata da iyalanta zuwa Bula Daloye bayan lalata sansanoninta.

ISWAP ta ƙone sansanonin JAS

Kara karanta wannan

Akwai ladar N60m: Sojoji sun saki hotuna da bayanan 'yan ta'adda 2 da ake nema

Bayanan sirrin sun ƙara bayyana cewa an ƙone Bula Murge da Nguro Bafuye, wurare biyu da mayaƙan JAS suka riƙa amfani da su a baya.

Rahoton ya ce hakan ya hana ƙungiyar amfani da muhimman mafaka da cibiyoyin gudanar da kayan aiki.

Har ila yau, bayanan sirrin sun nuna cewa wannan sabon rikicin ya ƙara raunana JAS a yankin, tare da samar wa jami'an tsaro damar ƙara kaimi wajen ayyukan yaƙi da ta'addanci.

An buƙaci dakaru su ƙara matsin lamba

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an shawarci dakarun da ke aiki a Miyanti, Bama, Kumshe da sauran yankunan da ke makwabtaka da su, da su yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da kai hare-hare.

An ce manufar ita ce hana ko wace daga cikin ƙungiyoyin sake haɗuwa ko kafa sababbin sansanonin aiki.

Haka kuma an shawarci kwamandojin sojoji su ci gaba da matsa wa ɓangarorin biyu lamba domin ƙara raunana ƙarfin yaƙinsu da kuma hana su samun damar gudanar da hare-hare a kudancin dajin Sambisa.

Rikicin ISWAP da JAS ya daɗe yana faruwa

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Wani bam ya fashe da ƴan ƙungiyar ISWAP yayin da suke hada shi

Wannan sabon artabu na daga cikin jerin rikice-rikicen da aka daɗe ana samu tsakanin ISWAP da JAS, waɗanda suka ci gaba da sauya yanayin ta'addanci a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Rikicin ya samo asali ne tun shekarar 2016 lokacin da ISWAP ta balle daga ƙungiyar Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Abubakar Shekau sakamakon sabanin ra'ayi da shugabanci.

Tun daga lokacin, ɓangarorin biyu suka riƙa fafatawa domin mallakar yankuna, hanyoyin karɓar haraji, ɗaukar sababbin mayaƙa da kuma muhimman maboyar da ke yankin Tafkin Chadi da dajin Sambisa.

'Yan Boko Haram da ISWAP sun gwabza fada a Borno
Shugaban rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Bam ya tashi da 'yan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mayakan ƙungiyar ISWAP guda biyar sun mutu sakamakon tashin wani abin fashewa a jihar Borno.

'Yan ta'addan sun mutu ne yayin da suke haɗa na'urorin fashewa na zamani (IED) a ƙauyen Maina Daya da ke ƙaramar hukumar Marte a Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng