Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukuncin Karshe kan Soke Rajistar ADC da Jam'iyyu 4
- Kotun daukaka kara ta soke hukuncin da ya umurci INEC ta cire ADC da wasu jam'iyyu hudu daga shafin rajistarta
- Alkalan kotun sun ce Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron karar saboda an shigar da ita ba bisa ka'ida ba
- Kotun ta tabbatar da cewa har yanzu ADC, APP, AA, ZLP da jam'iyyar Accord na ci gaba da kasancewa halastattun jam'iyyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja – Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta cire jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyun siyasa hudu daga rajista.
Kotun ta yanke hukuncin ne a zaman da alkalai uku suka gudanar, inda suka bayyana cewa umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar a ranar 15 ga Yuni ba shi da inganci a gaban doka.

Source: Twitter
Kotu ta kalubalanci shari'ar soke ADC
A hukuncin da Mai Shari'a Abba Mohammed ya karanta, kotun ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ta dauki shari'ar alhali ba ta da hurumin yin hakan, in ji rahoton Vanguard.
Ta ce karar da kungiyar tsofaffin 'yan majalisar dokoki ta tarayya (NFFL) ta shigar ba ta cika ka'idojin doka ba, domin an gabatar da ita ne ta wata kungiya da ba ta da matsayin shari'a.
Kotun ta kara da cewa babu wata ingantacciyar kara da za ta ba da damar fitar da umarnin da ya bukaci INEC ta soke rajistar jam'iyyun siyasar.
An yi watsi da hujjojin jam'iyyun siyasa
Kotun daukaka karar ta ce alkalin kotun farko bai yi cikakken nazari kan hujjojin da aka gabatar masa ba.
Ta ce an yi watsi da shaidun da suka nuna cewa jam'iyyun da ake kara sun taba samun kujeru a zabukan da suka gabata, abin da ya nuna sun cika sharuddan da kundin tsarin mulki ya tanada.
Kotun ta kuma bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ta ci gaba da sauraron shari'ar duk da umarnin dakatar da ita da kotun daukaka kara ta bayar tun farko.
Kotun ta soki alkalin Babbar Kotun Tarayya
Kotun ta ce alkalin Babbar Kotun Tarayya ya yi kunnen uwar shegu da umarnin da aka ba shi na dakatar da shari'ar har sai an kammala sauraron daukaka kara.
Saboda haka, ta ce abin da ya dace shi ne kotun ta yi watsi da karar tun farko saboda rashin hurumi da kuma rashin cancanta.
A sakamakon haka, kotun ta amince da daukaka karar da jam'iyyun siyasar suka shigar tare da umurtar kungiyar NFFL ta biya kudin shari'a.

Source: Twitter
Jam'iyyun da hukuncin ya shafa
Jam'iyyar Punch ta rahoto cewa baya ga jam'iyyar ADC, sauran jam'iyyun da kotun ta tabbatar da ci gaba da kasancewarsu a rajista sun hada da APP, AA, Accord (AP) da kuma ZLP.
A baya dai kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya tun ranar 16 ga Yuni, tare da sukar alkalin kotun bisa saba wa tsarin matakan shari'a.
Kotun ta bayyana cewa ci gaba da yanke hukunci duk da umarnin dakatar da shari'ar wani nau'in raina ikon kotu ne, tana mai tuna cewa Kotun Koli ta taba bayyana irin wannan hali a matsayin abin da bai dace da alkalin da ke kan kujerar shari'a ba.
An dakatar da soke rajistar ADC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin babbar kotun tarayya da ya umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu.
Alkalan kotun sun umarci hukumar INEC da ta jira a kammala sauraron karar da ke gabanta kafin daukar wani mataki kan jam’iyyun.
Kotun ta soki hukuncin da kotun tarayya ta yanke, tana mai bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa tsarin shari’ar Najeriya.
Asali: Legit.ng


