"Sojoji Kadai ba Za Su Iya ba"; Sarkin Potiskum Ya Fadi Hanyar Magance Matsalar Tsaro a Najeriya

"Sojoji Kadai ba Za Su Iya ba"; Sarkin Potiskum Ya Fadi Hanyar Magance Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Mai martaba Sarkin Potiskum ya ce ba za a kawo ƙarshen matsalar tsaro da amfani da ƙarfin soja kaɗai ba
  • Babban basaraken ya buƙaci gwamnati ta magance talauci, rashin adalci da sauran matsalolin zamantakewa da ke haddasa rikice-rikice
  • Ya jaddada cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da warware rikice-rikicen al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Potiskum, Yobe - Mai Martaba Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya bukaci shugabannin Najeriya su rungumi hanyoyin da suka fi haɗa kan jama'a wajen magance matsalar tsaro.

Sarkin ya ce amfani da ƙarfin soja kaɗai ba zai iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta ba.

Sarkin Potiskum ya ba gwamnati shawara
Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya Hoto: Umar Isa Adamu
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Sarkin Potiskum ya bayyana cewa bambance-bambancen da ke akwai a Najeriya na daga cikin manyan ƙarfinta yayin da yake magana kan halin da kasa take ciki.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan yaran da ake ba horo kan jirage marasa matuka

Ya kuma bukaci gwamnatoci a matakai daban-daban su magance talauci, rashin adalci da sauran matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke haddasa rikice-rikice a faɗin ƙasar.

Ya bayyana makamin da Najeriya ke da shi

"Najeriya ƙasa ce mai sarkakiya amma cike da kyawawan bambance-bambance, tana da ƙabilu sama da 300, kowacce da al'adunta da harshenta."
"Bai kamata a ɗauki bambance-bambance a matsayin rauni ba. Su ne babban ƙarfinmu. Ya dace kowane ɗan Najeriya ya ji cewa yana da gurbi a ƙasarsa, domin hakan yana ƙarfafa haɗin kan jama'a wajen ci gaban ƙasa." In ji shi

Ya yi magana kan matsalar tsaro

Game da matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar, Sarkin ya ce dole ne gwamnati ta wuce amfani da ƙarfi idan tana son samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

"Ba za a magance matsalar tsaro da amfani da ƙarfi kaɗai ba. Dole ne shugabanni su magance tushen matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke haddasa rikice-rikice cikin gaskiya da adalci." In ji shi

Ya ƙara da cewa shugabannin ƙasa su riƙa kallon kansu a matsayin iyaye ga dukkan 'yan ƙasa ba tare da la'akari da bambancin ƙabila, addini ko ra'ayin siyasa ba.

Kara karanta wannan

An goyi bayan harbe 'yan ta'adda da zarar an gan su ba tare da jiran izini ba

"Shugaban ƙasa nagari ya kamata ya zama kamar uba nagari, yana sauraron kowane ɗansa ba tare da nuna wariya ba, yana gyara kuskure cikin hikima tare da tabbatar da cewa kowa yana jin ana daraja shi. Idan shugabanni suka fifita jin daɗin al'umma a kan muradunsu na kashin kansu, ƙasa za ta samu ci gaba mai ma'ana."

Rawar sarakunan gargajiya wajen zaman lafiya

Sarkin Potiskum ya kuma jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen inganta zaman lafiya da hana rikice-rikicen al'umma.

"Saboda muna rayuwa tare da jama'a, mun fi sanin matsalolinsu kai tsaye. Wannan yana ba mu damar ba gwamnati shawara, sauƙaƙa tattaunawa cikin lumana da kuma warware matsalolin cikin gida kafin su ta'azzara."
"Ya kamata sarakunan gargajiya su jagoranci ci gaban al'umma, su bunƙasa ilimi, su tallafa wa harkokin tattalin arziki tare da inganta zaman lafiya." In ji shi.

A ƙarshe, Ibn Wuriwa Bauya ya bukaci shugabannin siyasa da na gargajiya su gudanar da mulki cikin adalci, riƙon amana da gaskiya.

Sarkin Potiskum ya ba gwamnati shawara
Taswirar jihar Yobe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun hallaka mutane a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai wani harin ta'addanci a jihar Sokoto inda suka kashe mutane.

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata a harin da 'yan bindigan suka kai a karamar hukumar Sabon Birni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng