'Yan Bindiga Sun Bi Mutane Har cikin Masallaci Sun Bindige Su a Sokoto
- Aƙalla mutum uku sun mutu a cikin masallaci yayin da ƴan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsamaye da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto
- Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun kwashe fiye da sa’o’i shida suna kashe mutane, sace jama’a, kwasar dabbobi da dukiyoyi
- Bayan harin na hatsabiban 'yan bindiga, an gano gawar mutum bakwai, yayin da aka tabbatar da sace aƙalla mutum uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Aƙalla mutum bakwai sun rasa rayukansu yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hari a jihar Sokoto
Hatsabiban 'yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Tsamaye da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Source: Original
Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata, inda suka ci gaba da kai hari har zuwa kusan ƙarfe 3:00 na safiyar ranar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kwashe fiye da sa’o’i shida suna kai farmaki kan mazauna ƙauyen, tare da sace mutane, kwasar dabbobi, wawashe dukiyoyi da harbe-harbe ba tare da tsari ba.
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mazauna ƙauyen sun gano gawar mutum bakwai da safiyar ranar Laraba bayan maharan sun bar yankin.
“Muna zaune bayan mun idar da sallar Isha’i ne sai ƴan bindigar suka shiga ƙauyenmu. Da farko sun kewaye jami’an tsaro da ke yankin sannan suka buɗe musu wuta."
“Sun mamaye wajen da jami’an tsaron suke, suka hana su fitowa. A lokaci guda, wasu daga cikin maharan suna bi gida-gida suna kwasar dabbobi, wawashe dukiyoyi da sace mutane.” In ji shi.
Majiyar ta ce mutum uku daga cikin waɗanda aka kashe sun mutu ne a cikin wani masallaci yayin harin.
Ya ƙara da cewa dukkansu mutanen da suka rasa matsugunansu ne, waɗanda suka tsere daga wasu ƙauyukan da ke makwabtaka saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga.
An ƙone mota da shaguna
Majiyar ta ce maharan sun kutsa cikin shaguna da dama, inda suka kwashe kayayyaki tare da ƙona wata mota da shaguna biyu kafin su bar ƙauyen.
Ya ce ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace nan take ba saboda mazauna yankin da dama sun tsere zuwa cikin daji yayin harin.
Mutanen ƙauyen da ƴan gudun hijira sun mutu
Majiyar ta bayyana cewa mutum biyu daga cikin waɗanda aka kashe ƴan asalin ƙauyen Tsamaye ne.
Sauran mutum biyar kuwa ƴan gudun hijira ne daga ƙauyukan da ke makwabtaka, waɗanda suka nemi mafaka a Tsamaye sakamakon hare-haren ƴan bindiga.
Ya ce an tabbatar da sace aƙalla mutum uku bayan danginsu sun kira lambobinsu ta waya, amma ƴan bindigar suka amsa tare da tabbatar da cewa mutanen suna hannunsu.
'Yan sanda sun yi bayani
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ta samu labarin harin amma tana jiran cikakkun bayanai.
“Mun samu labarin faruwar lamarin, amma har yanzu ba mu samu cikakkun bayanai ba yayin da muke jiran su.” In ji shi.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun kashe Kanal na soja
A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga sun kashe Kanal Abdussalam Ude, wani jami’i mai aiki a rundunar sojojin Najeriya a Abuja.
'Yan bindigan wadanda ke dauke da makamai sun kuma harbi matarsa a gidansu da ke yankin Kurudu na babban birnin tarayya, Abuja.
Asali: Legit.ng


