Saudi Ta Hada kai da Kasashen Musulmi 2 kan Tsaro, Iran na Gefe
- Yariman Saudi, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, da Firayim Ministan Pakistan Shehbaz Sharif za su sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro
- Majiyoyi sun bayyana cewa sauye-sauyen da ake samu ta fuskar tsaro da tashin hankali a yankin Gabas Tsakiya ne suka hanzarta cimma wannan kawance tsakaninsu
- Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Saudi Arabia ke fuskantar hare-haren jiragen sama marasa matuki da aka harbo daga yankin kasar Iraki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jeddah – Ƙasashen Saudi Arabia, Turkiyya, da Pakistan na daf da sanya hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa a birnin Jeddah ranar Juma'a, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas Tsakiya.
Yariman mai jiran gado na Saudi Arabia, Mohammed bin Salman, Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif za su jagoranci sanya hannu kan takardun kawancen.

Source: Getty Images
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito wata majiya ta kusa da rundunar sojin Saudi Arabia tana cewa ƙasashe uku na Musulmi sun dade suna tattaunawa kan samar da wannan kawance domin ƙarfafa tsaro.
Bayani kan yarjejeniyar
Rahoton Roya News ya bayyana cewa majiyar ta bayyana cewa a yau Juma'a ne ake sa ran za su rattaba hannu kan yarjejeniyar.
"Saudi Arabia, Pakistan, da Turkiyya za su sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa a ranar Juma'a a Jeddah.
"Tattaunawar ta ɗauki lokaci mai tsawo, amma al'amuran da suka faru kwanan nan a yankin ne suka hanzarta shirin."
Firayim Ministan Pakistan, Shehbaz Sharif, tare da Shugaban Rundunar Sojin ƙasar, Asim Munir, sun isa Saudi Arabia tun ranar Alhamis, yayin da Shugaba Erdoğan na Turkiyya ke shirin isowa ranar Juma'a.
Tun a shekarar 2025, ƙasashen Saudi Arabia da Pakistan ke da yarjejeniyar tsaro tsakaninsu, wadda ta tayar da jita-jita game da yiwuwar haɗin gwiwa kan tsarin makaman nukiliya domin ƙasar Pakistan na da makaman nukiliya.

Source: Getty Images
Hare-haren sun karu a yankin
Sanya hannun kan yarjejeniyar na zuwa ne sakamakon farmakin da Saudi Arabia ta ce ta fuskanta na jiragen sama marasa matuka da aka harbo daga ƙasar Iraki zuwa wuraren man fetur da ke Riyadh da Yankin Gabashin ƙasar.
Ma'aikatar Tsaron Saudi Arabia ta bayyana cewa ta sami nasarar ruguza jiragen, inda ta zargi ƙungiyoyin tsagera masu goyon bayan Iran da ke Iraki da ƙaddamar da hare-haren.
Iraki ta buƙaci a gudanar da bincike kan ikirarin Saudi Arabia, yayin da hukumomin Riyadh suka buƙaci gwamnatin Iraki da ta hana amfani da yankinta wajen ƙaddamar da hare-hare kan ƙasar.
Najeriya ta yi hadaka da Saudi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Najeriya ta haɗa gwiwa da Saudi Arabia da sauran ƙasashe 12 wajen goyon bayan kawancen tsaron teku na ƙasa da ƙasa domin kare hanyoyin kasuwanci da na man fetur a Tekun Maliya.
Wannan mataki ya sanya Najeriya a cikin tsarin tsaro na shiyar Gabas Tsakiya wanda Saudi Arabia ta ƙirƙiro domin haɗa ƙasashe kusan 50 sakamakon ƙaruwar hare-hare kan jiragen ruwan kasuwanci da tankokin mai.
Duk da cewa an gayyaci ƙasashe 51 zuwa taron, ƙasashe 43 ne kawai suka tura wakilansu, inda ƙasashe 14 kacal suka sanya hannu kan takardar amincewa da kafa wannan kawance.
Asali: Legit.ng


