Dangote Zai Yi Sadaka da Dukiyarsa, 'Yarsa Ta Bayyana Kason da Ya Ware

Dangote Zai Yi Sadaka da Dukiyarsa, 'Yarsa Ta Bayyana Kason da Ya Ware

  • Halima Dangote ta ce Aliko Dangote ya tanadi bayar da kaso mao tsoka na dukiyarsa ga ayyukan jin ƙai a cikin wasiyyarsa
  • An ce iyalansa sun amince da wannan tsari domin tabbatar da ayyukan gidauniyar sun ci gaba har zuwa al'ummomi masu zuwa
  • Idan aka yi la'akari da dukiyarsa ta yanzu, gudummawar za ta kai kusan dala biliyan 11.7 wadda za a rika taimakawa al'umma da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, ya shirya bayar da kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa ga ayyukan jin ƙai a matsayin wani ɓangare na tsarin rabon gadonsa.

'Yarsa, Halima Dangote, wadda take ɗaya daga cikin amintattun mambobin Gidauniyar Aliko Dangote, ta bayyana hakan.

Dangote zai sadakar da dukiyarsa
Hamshakin attajiri, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Halima Dangote ta bayyana hakan ne a wata hira da tashar Bloomberg tv wadda aka wallafa ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Tsaro: Tsohon daraktan DSS ta dura kan Pantami, ya faɗi illar naɗa shi minista

Ta ce Dangote ya samu amincewar iyalansa na ware kashi 33 na dukiyarsa domin ayyukan alheri da taimakon jama'a.

A cewar Bloomberg Billionaires Index, dukiyar Dangote ta kai kimanin dala biliyan 35.1. Idan aka ci gaba da wannan ƙima, kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa zai kai kusan dala biliyan 11.7.

Dalilin ware kaso ga gidauniya

Halima ta bayyana cewa mahaifinta yana kallon ayyukan jin ƙai a matsayin ginshiƙin abin da zai bari a baya, saboda haka ya saka su cikin tsarin rabon gadon iyali na dogon lokaci.

"Ya riga ya tsara komai ta yadda muka fi mayar da hankali kan lafiya da ilimi. Tun farko ya ba gidauniyar kashi 25 cikin 100 na dukiyarsa. Idan aka duba yadda dokar Shari'a ta Musulunci ta tanada, ya ba da kashi 33 cikin 100 na duk abin da zai bari ga gidauniyarsa."
"Wannan yana nuna muhimmancin da yake bai wa ayyukan jin ƙai, domin yana son su ci gaba."
"Mayar wa al'umma wani ɓangare na abin da muka samu yana cikin abin da muke yi. Mun yi imanin kasuwancinmu ya samu nasara ne saboda bayar da gudummawa da ayyukan alheri. Wannan ne ya sa kashi 33 cikin 100 yake da muhimmanci."

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

"Shi ya sa ya sanar da wannan kuduri, sannan ya nemi ni, 'yan'uwana mata biyu da mahaifiyarsa mu sanya hannu a ƙarƙashin wannan wasiyya domin tabbatar da cewa zai iya ba da wannan kaso ga bil'adama."

Halima Dangote

Gidauniyar Dangote ta karɓi ƙarin kuɗaɗe

Wannan sabon shiri ya ƙara gina kan ayyukan jin ƙai da Dangote ke yi ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, wadda aka kafa a shekarar 1994.

Halima ta ce an zuba dala biliyan 1.25 a cikin gidauniyar kusan shekara 10 da suka wuce, sannan daga baya aka ƙara mata dala miliyan 700.

Ta bayyana cewa kusan kashi 70 na kuɗaɗen da gidauniyar ke kashewa ana amfani da su ne a Najeriya, yayin da kashi 20 ke tallafa wa ayyuka a sauran ƙasashen Afirka, sauran kuma ana amfani da su a wasu sassan duniya.

Dangote ya ware wani kaso na dukiyarsa
Alhaji Aliko Dangote na jawabi a wajen taro Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Ayyukan gidauniyar sun shafi fannoni da dama

Ayyukan gidauniyar sun haɗa da lafiya, ilimi, abinci mai gina jiki da agajin jin ƙai.

Har ila yau, gidauniyar ta yi haɗin gwiwa da Bill & Melinda Gates Foundation da kuma gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya wajen yaƙi da cutar shan inna, lamarin da ya taimaka wajen kawar da cutar shan inna ta daji a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Dangote ya koma sayar da fetur a Naira

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da ke Legas ta koma sayar da man fetur da Naira bayan ta dakatar da tsarin.

Sai dai dawowar ta zo ne tare da ƙarin farashin fetur, inda aka ɗaga farashin daga N1,075 zuwa N1,215 kan kowace lita, wanda ya nuna ƙarin N140 ko kuma 13.02%.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng