An Bayyana Babban Abin da Ya Haddasa Ayyukan Daba a Jihar Kano
- Shugaban kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi a Kano ya ce shaye-shaye na kara yawaitar laifuffuka
- Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce gwamnati za ta dakile safarar miyagun kwayoyi tare da hukunta masu laifi
- Ya bukaci iyaye da al'umma su taimaka wajen kare matasa daga fadawa harkar shaye-shaye domin inganta al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jihar Kano – Shugaban Kwamitin Musamman na Jihar Kano kan Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Haramtattun Abubuwa, Barrista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi bayani.
Muhuyi ya bayyana cewa shan miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa aikata laifuffuka da rikice-rikicen kungiyoyin daba a jihar.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Muhuyi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, 28 ga watan Yulin 2026.
Ya ce karuwar shaye-shaye, safarar miyagun kwayoyi ba bisa ka'ida ba da kuma rikice-rikicen kungiyoyin daba ne suka sa gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin ta hanyar umarnin zartarwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu.
Ayyukan da aka dorawa kwamitin
Muhuyi ya ce aikin kwamitin ya hada da dakile hanyoyin shigowa da miyagun kwayoyi, gyaran masu shaye-shaye ta hanyar cibiyoyin gyaran hali da kuma tabbatar da gurfanar da masu safarar miyagun kwayoyi a gaban kotu.
"Shan miyagun kwayoyi wata babbar annoba ce da ke addabar al'ummarmu. Aikinmu shi ne mu toshe hanyoyin da ake shigo da wadannan kwayoyi, mu gyara wadanda suka fada cikin shaye-shaye ta hanyar cibiyoyin gyaran hali, sannan mu tabbatar an gurfanar da masu safarar su a gaban kotu."
- Muhuyi Magaji
Alakar shan kwayoyi da aikata laifi
Muhuyi ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka, jaridar The Punch ta kawo labarin.
A cewarsa, mutane da dama kan aikata sata, tashin hankali da sauran laifuffuka yayin da suke karkashin tasirin kwayoyi.
"Shan miyagun kwayoyi na tafiya tare da aikata laifi. Idan mutum yana karkashin tasirin kwayoyi, ya kan aikata sata, tashin hankali da sauran laifuffuka."
- Muhuyi Magaji
Rikicin daba na da nasaba da shaye-shaye
Shugaban kwamitin ya kuma danganta ayyukan kungiyoyin daba da shan miyagun kwayoyi.
Ya ce a lokuta da dama rikice-rikice da hare-haren ramuwar gayya tsakanin wadannan kungiyoyi na faruwa ne sakamakon tasirin kwayoyi.
"Matsalar daba ta samo asali ne daga shan miyagun kwayoyi. A mafi yawan lokuta, rikice-rikice da hare-haren ramuwar gayya tsakanin wadannan kungiyoyi na da nasaba da tasirin kwayoyi."
- Muhuyi Magaji

Source: Original
Ya soki tsoma bakin iyaye da 'yan siyasa
Muhuyi ya nuna damuwa kan yadda wasu iyaye da 'yan siyasa ke kokarin kare wadanda ake zargi da aikata laifi domin kada su fuskanci hukunci.
Ya ce irin wannan tsoma baki na iya kawo cikas ga kokarin magance matsalar tsaro a jihar.
"Abin takaici ne yadda wasu iyaye ke nacewa cewa 'ya'yansu ba su da laifi ko da an kama su suna aikata laifi. Haka kuma wasu 'yan siyasa kan yi kokarin ganin an saki wadanda ake zargi. Dole ne a dakatar da hakan."
- Muhuyi Magaji
'Yan daba sun hallaka dan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan daba sun hallaka wani dan sanda da ke aiki a ofishin 'yan sanda na Hotoro a jihar Kano.
Jami'in dan sandan ya rasu ne lokacin wani fada da aka yi tsakanin ƙungiyoyin ’yan daba masu adawa da juna a Kano, saura watanni kaɗan ya yi ritaya.
Asali: Legit.ng


