Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Borno ta yi martani kan ikirarin cewa an biya 'yan ta'addan Boko Haram kudin fansa kafin kubutar da mutane 360 da aka yi garkuwa da su.
Tsugunne ba ta kare ba tsakanin shugabannin jam'iyyar NDC a Kano da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Sun zarge shi da yin kaka-gida kan komai a jam'iyyar.
Hukumar LASERC ta bayyana sunayen kamfanoni 38 da suka hada da MTN da Flour Mills da suke gudanar da ayyukan samar da lantarki a jihar Legas ba da izini ba.
Hauhawar farashin gas a Abuja ya tilasta wa gidaje da masu sana’o’in abinci komawa amfani da gawayi da itace yayin da mazauna suka bukaci gwamnati ta dauki mataki.
An kai wani hari a wasu garuruwa da ke tsakiyar Israila. Jami'an ba da agajin gaggawa sun tabbatar da asarar rai tare da kai mutanen da suka jikkata zuwa asibiti.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto fararen hula da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a Borno. An ba mutanen da aka ceto kulawar da ta dace.
Matashin dan wasa, Zadok Yohanna, ya kafa tarihi bayan ya koma kungiyar Brighton & Hove Albion ta kasar Ingila. Ya doke tarihin da Mikel Obi ya taba kafawa.
'Yan bindiga dauke da makamai sum yi jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) kwanton bauna a jihar Kebbi. 'Yan bindigan sun kashe jami'ai 3 a harin.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya bayyana cewa wasu gwamnonin jam'iyyar APC na zawarcinsa domin ya koma cikinta biyo bayan barin ADC.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari