Matashin Dan Wasan Najeriya Ya Doke Mikel Obi, Ya Kafa Sabon Tarihi
- Matashin dan wasan gaba, Zadok Yohanna, zai taka leda a kungiyar Brighton $ Hove Albion ta kasar Ingila
- Dan wasan wasan yake dan asalin jihar Kaduna ne, zai yi wasa a kungiyar ne bayan an sayo shi daga tsohon kulob dinsa na AIK Stockholm
- Kudin da kungiyar Brighton ta zare domin sayo Zadok Yohanna, sun sanya ya doke tarihin da Mikel Obi ya kafa a shekarar 2006
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Burtaniya - Ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ke wasa a gasar Premier League ta ƙasar Ingila, Brighton & Hove Albion, ta sayi matashin dan wasan Najeriya, Zadok Yohanna.
Kungiyar Brighton & Hove Albion ta dai kashe fam miliyan £21.5 wajen sayen matashin ɗan wasan gaba na Najeriya, Zadok Yohanna, daga ƙungiyar AIK Stockholm.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Zadok Johanna wanda dan asalin jihar Bauchi ne ya shiga harkar ƙwallon ƙafa ta kwarruwa kuma ya koma Turai a shekarar da ta gabata.
Zadok Yohanna ya kafa tarihi
Zadok Yohanna ya zama ɗan wasa mafi tsada da ya taɓa komawa daga ƙasar Scandinavia zuwa ɗaya daga cikin manyan rukunonin gasar ƙwallon ƙafa a Turai.
Ɗan wasan mai shekaru 18 wanda ke taka leda a ɓangaren hagu ko dama ya kuma zama matashi ɗan Najeriya mafi tsada, inda ya doke kuɗin canjin sheka na John Obi Mikel zuwa Chelsea daga ƙungiyar Lyn Oslo ta ƙasar Norway a shekarar 2006.
Brighton, wadda ta doke Newcastle United da Chelsea wajen samun sa hannun matashin ɗan wasan mai sauri da dabarun gaske, ta bayyana cewa ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar, kuma zai kasance da ƙungiyar har zuwa shekarar 2031, Fabrizio Romano ya kawo labarin.
An yaba da kwarewar Zadok.Yohanna
Matashin babban mai horarwa na Brighton, Fabian Hurzeler, ya bayyana sha'awarsa da yabo mai yawa ga Yohanna, sannan ya bayyana cewa zai shiga cikin babbar ƙungiyar ta farko nan take.

Kara karanta wannan
Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe
“Ina ɗokin fara aiki tare da Zadok. Bayan na kalli wasanninsa da fasahohinsa, shi ɗan wasa ne da zai iya kawo sauyi a wasanni a fagen gaba."
“Har yanzu shi matashi ne, kuma zai buƙaci lokaci domin ya saba da ƙungiyar da kuma gasar Premier League, amma shi ɗan wasa ne mai ban sha'awar kallo kuma yana ɗauke da irin ƙirƙirar dabarun da muka sani magoya bayanmu za su ji daɗinsa."
“Yana da kuzari, yana da gudu, kuma yana son fuskantar 'yan wasa. Fasahohinsa da ikonsa za su kasance gagarumin ƙari ga zaɓuɓɓukanmu na farmaki.”
- Fabian Hurzeler

Source: Twitter
Zadok na son gasar Premier League
Zadok Yohanna ya kuma bayyana sha'awarsa ga gasar EPL kuma yana kallon Brighton a matsayin ƙungiyar da ta dace da ci gabansa duba da mutuncin ƙungiyar na haɓaka matasan taurari.
Yohanna, wanda ya kammala karatu daga makarantar horarwa ta Ikon Allah Academy, ya zura ƙwallaye biyar tare da bayar da taimako aka zura ƙwallaye guda huɗu a cikin wasanni 18 kafin canjin shekarsa na ba-zata zuwa ƙasar Ingila.
Tsohon dan wasan Najeriya ya rasu

Kara karanta wannan
Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan wasan tsakiya na Najeriya, Henry Nwosu, ya yi bankwana da duniya bayan rashin lafiya.
Tsohon abokin wasansa, Segun Odegbami ya bayyana cewa Nwosu ya rasu bayan kwanaki biyar yana kwance a asibiti yana fama da rashin lafiya.
Ya ce marigayin ya rasu da misalin karfe 4:00 na safiya a asibitin koyarwa na Jami'ar Lagos da ke Ikeja a Legas.
Asali: Legit.ng
