Yadda Sojoji Suka Yi Wa 'Yan Boko Haram Dabara wajen Ceto Mutane 360 da Aka Sace a Borno

Yadda Sojoji Suka Yi Wa 'Yan Boko Haram Dabara wajen Ceto Mutane 360 da Aka Sace a Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutanen da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza
  • Dakarun sojojin sun ba da kulawa ta hanyar duba lafiyar mutanen da aka kafin mika su ga iyalansu da suka dade cikin jimamin rashinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin kasan Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun sanar da ceto fararen hula guda 360 daga hannun 'yan ta'adda a jihar Borno.

Sojojin sun ceto mutanen ne da yawansu mata da yara ne, waɗanda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su daga garinsu na Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Sojoji da dama sun mutu da 'yan ta'adda suka bude wuta ana ruwan sama a Borno

Sojoji sun ceto mutanen da aka sace a Borno
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya da wasu daga cikin mutanen da aka sace Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin jami'in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta Gabas ta Tsakiya, Laftanar Kanal Haruna M Sani, ya fitar a shafin X.

Sojoji sun sanya 'yan ta'adda cikin rudani

Aikin ceton ya biyo bayan wani shiri na musamman da aka gudanar ta ɓangarori mabanbanta a kewayen duwatsun Mandara a ranar Asabar, 6 ga watan Yunin 2026.

A cewarsa, dakarun ayyuka na musamman sun fara gudanar da wasu ayyukan share fage waɗanda suka haifar da ruɗani a cikin sansanonin 'yan ta'addan, hakan ya buɗe wa dakarun ƙasa na26 Task Force Brigade hanyar kwaso mutanen da aka tsare cikin nasara.

An ceto mutanen Ngoshe da aka sace

“Fararen hula da aka ceto suna cikin mazauna garin da aka sace a lokacin harin ta'addanci da aka kai a garin Ngoshe ranar 3 ga Maris, 2026.”

“Sai dai kuma, aikin ya samu koma-baya na baƙin ciki yayin da jarirai biyu suka rasu a lokacin ƙoƙarin ceton sakamakon tsananin wahala da sarkakiyar yanayin da aka fuskanta yayin jigilar waɗanda abin ya shafa zuwa wuri mai aminci."

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu nasara kan 'yan ta'adda, an kashe tsageru da ceto mutanen da aka sace

- Laftanar Kanal Haruna M Sani

Ya ƙara da cewa dukkan mutanen da aka ceton sun fuskanci binciken lafiya na gaggawa da isarsu, yayin da waɗanda ke buƙatar kulawar lafiya ta gaggawa jami'an lafiya suka daidaita yanayin jikinsu sannan aka kwantar da su a babban asibitin Gwoza domin yi masu magani.

Sojoji sun ceto mutane a Borno
Sojoji na duba lafiyar mutanen da aka ceto a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An tabbatar da ceto mutanen

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kungiyar Matasan Borno ta Kudu (BOSYA), Samaila Kaigama, shi ma ya tabbatar da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ɗin.

A cewar Kaigama, ƙungiyar ta taka rawar sulhu wajen tabbatar da sakin waɗanda abin ya shafa ta hanyar ci gaba da tattaunawa da sadarwa mai dorewa.

Ya bayyana cewa:

“Mun tabbatar da sakin dukkan mata da yara guda 416 daga Ngoshe. An sake su ne a ranar 6 ga Yunin 2026."

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne sun kashe sojoji a wani sansanin soja da ke Mandara-Girau, a karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

PDP ta kara birkicewa, 'yan majalisa 4 na jam'iyyar daga Bauchi sun koma APM

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun bude wa dakarun sojojin wuta ba zato ba tsammani a yayin da ruwan sama mai karfi ke sauka.

Maharan sun zo ne da yawan gaske, lamarin da ya sa suka yi nasarar mamayar sojojin ba zato ba tsammani tare da jawo asarar rayuka mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng