Amurka Ta Gamu da Matsala, Jirgin Yakinta Ya Rikito a Kusa da Mashigar Hormuz

Amurka Ta Gamu da Matsala, Jirgin Yakinta Ya Rikito a Kusa da Mashigar Hormuz

  • Wani jirgin helikofta na yaki kirar Apache na rundunar sojojin Amurka, ya rikito daga sararin samaniya a kusa da mashigar ruwa ta Hormuz
  • Wasu mutanen da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa an samu nasara wajen ceto ma'aikatan da ke cikin jirgin lokacin da ya fadi
  • Ana dai amfani da jirgin ne mafi yawan lokuta wajen aikin sintiri yayin da rundunar sojojin Amurka ke ci gaba da kulle tashoshin jiragen ruwan Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Wani jirgin helikofta na yaƙi ƙirar Apache na rundunar sojan kasa ta Amurka ya faɗi kusa da Mashigar ruwan Hormuz.

An ceto ma'aikata biyu da ke cikinsa lafiya, kamar yaddda mutane biyu da aka yi musu bayani kan lamarin suka bayyana.

Jirgin yakin Amurka ya fado
Jirgi yakin Amurka a sararin samaniya Hoto: Jalaa Marey
Source: Getty Images

Tashar New York Times ta kawo rahoton fadowar jirgin na sojojin Amurka a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya gamu da hatsari har an mutu a layin Warri, Itakpe

Me ya kakkabo da jirgin yakin Amurka?

Ba a bayyana nan take ba ko makaman dakarun Iran ne ya kakkabo jirgin na Apache, ko matsalar inji ya samu, ko kuma ya fuskanci wata matsalar daban ba, jaridar Jerusalem Post ta kawo labarin.

Daya daga cikin mutanen da ya bayyana lamarin, wanda ya yi magana da sharaɗin sakaya sunansa ya kuma ce ana tsaka da gudanar da bincike kan lamarin.

Lamarin ya auku ne bayan fuskantar hare-hare a yankin sannan daga baya suka lafa, yayin da Isra'ila da Iran suka yi musayar hare-haren soja kafin su ja da baya.

Hare-haren sun kasance misali na baya-bayan nan na yanayin rashin tabbas da ke tattare da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ana amfani da jirgin Apache a yaki da Iran

Rundunar CENTCOM ta Amurka tana amfani da jiragen helikofta na Apache, har ma da jiragen yaƙi na zamani da jirage marasa matuƙi, a matsayin ɓangare na ƙoƙarin Amurka na budewa tare da kawo ƙarshen kulle mashigar Hormuz da Iran ta yi.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

Wannan shi ne karon farko da wani jirgin Apache ya fado tun lokacin da aka fara yaki tsakanin Amurka da Iran a watan Fabrairu, inda Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma ta yi iƙirarin kakkabo jiragen marasa matuƙi ƙirar MQ-9 Reaper guda 30 a lokacin yakin.

Jirgin yakin Amurka ya rikito daga sama
Jirgin yakin Amurka kirar Apache Hoto: Abdel Majid Bziouat
Source: Getty Images

Gabaɗaya ana amfani da jiragen na Apache ne don ayyukan sintiri, amma sun kasance suna ƙara shiga cikin yankin Iran a matsayin wani ƙoƙari na nuna karfi daga ɓangaren CENTCOM.

Shugaban Amurka ya yi barazanar kyale Netanyahu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kara janye jiki daga taimakawa Isra'ila a takaddamar da ake a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban na Amurka ya yi gargadin ba zai taya Isra'ila yaki da kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, yayin da ya yi magana da Benjamin Netanyahu ta wayar tarho.

Donald Trump ya gargaɗi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa zai iya tsinci kansa yana yaƙi shi kaɗai idan Isra’ila ta koma yaƙi da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng