An Shiga Firgici da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Jami'an FRSC a Kebbi

An Shiga Firgici da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Jami'an FRSC a Kebbi

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun shammaci wasu jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Tsagerun 'yan bindigan sun yi wa jami'an na hukumar FRSC lokacin da suke gudanar da ayyukansu a karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi
  • Jami'an na hukumar FRSC sun yi kokarin tserewa domin tsira da rayukansu, amma sai 'yan bindigan suka bi sawunsu tare da bude masu wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe wasu jami'ai uku na hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) a jihar Kebbi.

'Yan bindigan sun kashe jami'an na hukumar FRSC ne yayin wani hari a karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi.

'Yan bindiga sun kashe jami'an FRSC a Kebbi
Shugaban hukumar FRSC na kasa, Shehu Mohammed Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sojoji da dama sun mutu da 'yan ta'adda suka bude wuta ana ruwan sama a Borno

'Yan bindiga sun kashe jami'an FRSC

Majiyoyin tsaro sun un bayyana cewa harin ya auku ne da misalin ƙarfe 12:55 na rana a ranar Alhamis, 4 ga watan Yunin 2026, yayin da jami'an ke kan gudanar da aikinsu a kan hanyar.

An bayyana cewa tsagerun maharan wadanda suke dauke da makamai sun yi wa ayarin jami'an na hukumar FRSC kwanton bauna ne.

Bayan hango maharan, an ruwaito cewa jami'an na FRSC sun yi ƙoƙarin tserewa, amma 'yan bindigan sun bi sawunsu a kan babura kuma suka buɗe musu wuta, inda suka kashe dukkan jami'an guda uku.

An bayyana sunayen jami'an da aka kashe

Waɗanda abin ya shafa an gano sunayensu a matsayin Umar Aliyu, mataimakin babban jami'in kiyaye hanya (DCRMA), Ezra Manu Gona, babban jami'in kiyaye hanya (SRMA), da kuma Mansur Ibrahim Nasir, jami'in kiyaye hanya na ɗaya (RMA I).

Lamarin ya ƙara rura wutar fargaba a yankin, inda majiyoyin tsaro suka ce an shawarci jami'an da su kasance masu taka-tsantsan har sai an kammala ƙarin binciken tantance tsaro.

Kara karanta wannan

"An kashe bayin Allah"; Mutane sun bar kauyukansu a Sokoto sakamakon hare haren 'yan bindiga

'Ya bindiga sun kashe jami'an FRSC a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukumomi na kokarin cafke masu laifi

Hukumomi sun bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin bin sawun waɗanda suka aikata laifin da kuma fayyace abubuwan da suka faru wajen aukuwar kwanton baunan da ya jawo asarar rayuka.

Dakarun tsaro sun tsananta sanya ido da sauran matakan riga-kafi a yankin da abin ya shafa domin hana ƙarin hare-hare da kuma dawo da kwanciyar hankali a kan hanyar.

'Yan bindiga sun kori mutane a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa hare-haren 'yan bindiga a jihar Sokoto sun tilastawa mutanen kauyuka da dama barin gidajensu.

Aƙalla mutane 52 ne aka kashe a hare-haren, ciki har da mutane 46 a kauyukan karamar hukumar Tureta da kuma wasu guda shida a karamar hukumar Sabon Birni.

Hare-haren sun haifar da raba mutane da muhallansu a faɗin yankin yayin da mazauna garin suka bar gidajensu kuma suka nemi mafaka a wurare mafi aminci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng