Masana'antar Fina Finai Ta Yi Rashi, Jarumin Fim Ya Yi Bankwana da Duniya
- Jarumi a masan'antae Nollywood Chijioke “Cjay” Nwokafor ya rasu, lamarin da ya jefa masana’antar fina-finan Najeriya cikin jimami
- Jaruma Nkechi Blessing ta sanar da rasuwar Cjay tare da soke fitar da sabon fim ɗinta domin girmama marigayin
- Cjay ya fara harkar fim a 2021, inda ya fito a fina-finai da dama kafin rasuwarsa, ciki har da Larry Cold da Mum Overnight
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Masana’antar fina-finan Najeriya ta shiga zaman makoki bayan rasuwar ɗan wasan Nollywood, Chijioke “Cjay” Nwokafor.
Jarumin na masana'antar Nollywood ya yi bankwana da duniya ne a ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026.

Source: Instagram
Abokiyar aikinsa, jaruma Nkechi Blessing, ce ta sanar da rasuwarsa a shafinta na Instagram ranar Laraba, inda ta wallafa wasu bidiyonta tare da marigayin.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Nkechi Blessing ta soke fitar da sabon fim
Jarumar ba ta bayyana abin da ya haddasa rasuwar Cjay ba, amma ta ce ta soke fitar da sabon fim ɗinta mai suna Egusi Ogbono domin girmama marigayin, wanda ya fito a cikin fim ɗin.
Da farko, an shirya fitar da fim ɗin da ƙarfe 5:00 na yamma ranar Laraba, amma Blessing ta janye shi bayan wani asibiti ya tabbatar da rasuwar Cjay.
Jarumar ta ce ta yi magana da Cjay da safiyar Laraba, kafin daga bisani ta samu labarin rasuwarsa.
“Cjay Nwoke Oma, shin da gaske shi kenan ka tafi? Mun yi tsare-tsare da yawa. Na yi magana da kai da ƙarfe 8:00 na safe yau, bayan wasu sa’o’i kuma ba ka ƙara kasancewa tare da mu ba,”
"Don Allah idan akwai yiwuwar ka dawo, ka dawo, domin na ƙi yarda in rubuta wani abu dabam. Wannan rashin ya yi mini yawa.” In ji ta.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, iyalan Cjay da abokan aikinsa ba su bayyana ƙarin bayanai kan rasuwarsa ba, kuma ba a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa ba.
Wanene Cjay Nwokafor?
Cjay ya fara sana’ar fim a shekarar 2021, inda ya samu damar fitowa a fina-finai da dama kafin rasuwarsa.
Ɗan wasan, wanda ya fito daga Jihar Anambra, ya taka rawa a fina-finai kamar Larry Cold, Mum Overnight da A Day to My Wedding.
A wata hira da ya yi da Trybe TV a ranar 21 ga Satumba, Cjay ya bayyana yadda fara aiki a wani shirin fim ya sa ya yanke shawarar shiga harkar wasan kwaikwayo a matsayin sana’a.
Ya ce ya yi aiki a wani shirin fim tare da mai shirya fina-finai Ruth Kadiri, inda yadda ya ga ’yan wasan kwaikwayo ke gudanar da kansu ya ƙara masa sha’awar shiga sana’ar.

Source: Instagram
Matar sarki a Gombe ta rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa matar Mai Kaltungo kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Gombe, Injiniya Saleh Muhammad Umar ta rasu.
Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Amina Saleh Muhammad ta rasu ne ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026 bayan gajeruwar rashin lafiya. :
Asali: Legit.ng
