'Dalilin da Ya Sa Jika na Ya Ƙi Amincewa Ya Yi Aiki da Ni': Dangote Ya Magantu
- Aliko Dangote ya bayyana cewa jikansa na farko, wanda injiniyan lantarki ne, ba ya son shiga kamfanin iyalinsu yanzu
- Ya ce jikan nasa na son samun gogewa a wasu ɓangarori musamman a harkokin kuɗi, kafin ya koma kamfanin Dangote
- Dangote ya ce ’ya’yansa mata uku, Mariya, Halima da Fatima, sun riga sun shiga harkokin gudanar da kamfanin iyalinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Nairobi, Kenya - Hamshakin attajirin Afirka kuma shugaban Dangote Group, Aliko Dangote, ya bayyana cewa jikansa na farko ba ya sha’awar aiki tare da shi a yanzu.
Dangote ya ce jikansa, wanda injiniyan lantarki ne, yana son samun ƙwarewar aiki a wajen kamfanin iyalinsu kafin daga bisani ya shiga kasuwancin kamfanin Dangote.

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani taron tattaunawa da masu zuba jari da aka shirya a Nairobi, Kenya, cewar Daily Trust.
Yadda jikan Dangote ya ki aiki da shi
A cewarsa, matashin injiniyan yana tunanin yin aiki da manyan kamfanonin ba da shawarar ƙwararru na duniya, KPMG ko PwC, domin samun ƙwarewa musamman kan harkokin kuɗi.
Da yake magana kan shirin maye gurbin shugabanci da kuma rawar da ’yan iyalinsa ke takawa a kamfanin, Dangote ya ce jikansa na son samun ƙwarewa a wajen kamfanin.
Ya ce:
“Jikana na farko, a yanzu ba ya ganin aiki tare da ni yana da ban sha’awa. Yana son zuwa KPMG ko PwC ya samu ƙwarewa. Daga nan zai dawo ya shiga kamfaninmu. Shi injiniyan lantarki ne, amma yana son fara koyon harkokin kuɗi.”
Dangote ya kuma gabatar da ’yarsa ta fari, Mariya Dangote, da mijinta Alassane, waɗanda suka halarci taron.
Ya gayyaci ma’auratan su miƙe domin su gaishe da mahalarta taron, yayin da ya bayyana Mariya a matsayin mutum mai kunya.

Kara karanta wannan
2027: Gwamna ya yi alƙawarin gyara Najeriya cikin shekaru 4 idan ya zama shugaban ƙasa

Source: UGC
Mukaman da ƴaƴan Dangote a kamfaninsa
Dan kasuwar ya ce ’ya’yansa mata uku, Mariya, Halima da Fatima, sun riga sun shiga gudanar da kasuwancin iyalinsu, inda suke riƙe da mukaman zartarwa a sassa daban-daban na kamfanin.
Ya ce tsara manyan manufofi na nesa sosai na iya sa ma’aikata da shugabanni su yi sakaci, saboda wa’adin cikar burin zai yi musu nisa, cewar Daily Post.
Maimakon haka, ya ce kamfanin ya fi amfani da tsare-tsaren shekaru biyar, wadanda manyan shugabanni da daraktoci a sassa daban-daban ke taka rawa wajen tsara su.
A baya, Dangote ya taba magana kan batun maye gurbin shugabanci a kamfanin, inda ya ce samun ɗa namiji ba shi ne abin da ya fi muhimmanci a gare shi ba.
Ya kuma bayyana cewa ɗaya ko fiye daga cikin ’ya’yansa mata na iya zama shugabannin kamfanin a nan gaba, yana mai cewa cancantar jagoranci ce ya kamata ta zama tushen zaɓen wanda zai gaji ragamar kamfanin, ba jinsi ba.
Dangote: Ana wayar da kan yan Arewa
An ji cewa kungiyar ACF ta gudanar da gangamin wayar da kan jama'a a jihar Kano kan sayen hannun jari na Matatar Dangote.
Kungiyar ta ce wannna aiki da ta fara na wayar da kai zai taimaka wa masu son zuba jari fahimtar yadda ake sayen hannun jarin.
ACF ta gargadi yan Najeriya da ke da niyyar zuba jari da su guji jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.
Asali: Legit.ng

