Mazauna Abuja Sun Nema wa Kansu Mafita da Farashin Gas din Girki Ya Kai N2000
- Hauhawar farashin gas din griki a Abuja daga N1,200 zuwa N2,000 ya sa gidaje da masu sana’o’i da dama komawa amfani da itace da gawayi
- Masu sana’ar abinci sun bayyana cewa karin kudin gas ya rage ribarsu matuka, lamarin da ya tilasta musu amfani da hanyoyin girki na gargajiya
- Mazauna birnin tarayya sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan dakile karin farashin saboda yadda yake kara tsadar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsananin tashin farashin iskar gas din girki ya fara shafarar rayuwar gidaje da ma masu sana'o'i a babban birnin tarayya Abuja.
Tashin gwauron zabin farashin ya tilasta wa gidaje da masu sana’o’i da dama komawa amfani da hanyoyin gargajiya kamar itace da gawayi domin yin girki.

Source: Getty Images
An samu karin farashin gas a Abuja
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa farashin gas a Abuja ya tashi daga kusan N1,200 zuwa N2,000 kan kowanne kilo cikin ‘yan watannin nan.
Wata mai sana’ar sayar da abinci a Gwarimpa da ke Abuja, Misis Mayo Akinpelu, ta ce ta daina amfani da gas saboda yawan karin farashinsa da ya zama barazana ga kasuwancinta.
A cewarta, yanzu ta koma amfani da itace da gawayi saboda sun fi saukin samu kuma ana iya sayensu kadan-kadan.
“Cika tukunyar gas ya zama abu mai wahala saboda farashinsa yana ta karuwa. Ba zan iya siya ba kuma in samu riba mai kyau. Yanzu tukunya mai cin kilo 12.5 tana kaiwa N25,000,” in ji Mayo.
Karin farashin ya rage ribar 'yan kasuwa
Wata mai sana’ar abinci a Dutse da ke karamar hukumar Bwari, Victory Samson, ta ce karin farashin gas ya rage ribarta sosai tare da kawo cikas ga harkokinta.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume ya jinjina wa Tinubu, ya ce 'yan Arewa za su saka masa da kuri'u a 2027
Ita ma wata ‘yar kasuwa a Kubwa, Misis Grace Oluwatimilehin, ta bayyana mamakinta kan sabon karin farashin bayan ta sayi gas a kan farashi mai sauki a baya-bayan nan.
“Ranar karshe da na sayi gas yana N1,600/kg, amma da na koma jiya sai aka ce ya koma N2,000/kg.
“Yanzu ina amfani da na'urar lantarki wajen girki, sannan wani lokacin ina amfani da gawayi da itace maimakon gas."
- Grace Oluwatimilehin.

Source: Getty Images
Martanin masana kan tsadar gas
Masana harkar iskar gas sun bayyana cewa karancin kaya, tashin kudin sufuri da matsin tattalin arziki na daga cikin abubuwan da suka haddasa karin farashin, in ji rahoton Punch.
Sun kuma ce matsalar canjin kudin waje da karin kudin shigo da kayayyaki sun kara dagula lamarin, lamarin da ya sa ‘yan kasuwa ke kara farashi domin gujewa asara.
A cewarsu, idan ba a dauki matakan gaggawa ba, karin farashin gas na iya tilasta wa karin gidaje komawa amfani da hanyoyin gargajiya na girki da ka iya haddasa matsalolin muhalli da lafiya.
Tashin farashin gas lokacin Sallah
A wani labari, Legit Hausa ta rahoto cewa ko a lokacin da ake shirin bukukuwan babbar Sallah, kungiyar NALPGAM ta nuna damuwa kan yadda ake fama da tashin farashin gas a Najeriya.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
A cewar ƙungiyar, yanzu farashin kilo daya na gas ya haura N1,500 yayin da ‘yan kasuwa ke sayen ton 20 na gas tsakanin N25.2m zuwa N26.2m.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa wasu dillalai ma suna sayar da kilo 1 na gas din girki tsakanin N1,600 zuwa N2,000, lamarin da ya jefa jama'a a mawuyacin hali.
Asali: Legit.ng
