Bello El Rufai Ya Ambaci ‘Yan Siyasan da Suka Tuna da Su da Aka Kama Mahaifinsu
- Mohammed Bello El-Rufai ya bayyana halin da mahaifinsu yake ciki sakamakon tsare shi da hukumomi su ke yi
- ‘Dan majalisar na Kaduna ta Arewa ya ce ‘yan siyasa irinsu Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso suna tare da su
- Hon. Bello El-Rufai ya yi godiya ta musamman ga Peter Obi, mutumin da a baya yana cikin masu adawa da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mohammed Bello El-Rufai ya yi tsokaci a game da halin da mahaifinsu, Nasir El-Rufai yake ciki a hannun hukuma.
Matashin ‘dan siyasar ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa musamman ‘yan adawa suna tare da su.

Source: Twitter
Bello El-Rufai yana wannan bayani da tashar Trust TV yi hira da shi, bidiyon yana yawo tun tuni a dandalin Instagram.
Maganar ‘dan majalisar wakilan tarayyan ta karyata zancen da ake yi cewa kusan kowa ya kaura cewa Malam El-Rufai.
Wadanda ba su manta da Nasir El-Rufai ba
A cikin wadanda ya ambata akwai Wazirin Adamawa wato Atiku Abubakar wanda yake takarar shugaban kasar 2027 a ADC.
Ya kuma hada da abokin gaminsa kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi a cikinsu
Hon. Bello El-Rufai ya ce Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya kira da jagora kuma uba yana tuntubarsu game da El-Rufai.
'Danuwan Bello wato Bashir El-Rufai yana cikin masu nuna kaunarsu ga jagoran Kwankwasiyya.
Peter Obi yana kiran iyalin El-Rufai
A bidiyon, an ji yadda Bello El-Rufai ya kebe Peter Obi da yabo na musamman saboda zumuncinsa.
Duk da Peter Obi yana jam’iyyar NDC shi kuma mahaifinsa yana ADC, yana yawan neman jin halin da Malam yake ciki.
Abin da ya fi kunyata matashin shi ne yadda ya yaki ‘dan takaran shugaban kasar a lokacin da adawa ta yi zafi a 2023.
“Ina so in gode masu, musamman Peter Obi. Yana yawan kira na ya tambaya game da baba na.
"Ni kuma da na ke shekara 38, lamarin Obi darasi ne wannan a rayuwa, ina yawan sukar shi."
- Bello El-Rufai
Lokacin da Bello El-Rufai ya yi takarar ‘dan majalisa a Kaduna, yana APC yayin da Obi yake neman mulkin kasar a inuwar LP.
Leadership ta rahoto shi yana bayanin yadda El-Rufai ya yi amfani da halin da yake ciki wajen rubutu da karance-karancen shi.
Shi kuma Malam, yana amfani da damar wajen karasa rubuta littafi, karanta Kur’ani da kuma izna kan abubuwan da suka faru.
Shawarar Babachir ga Obi/Kwankwaso
Kwanaki da shigowa NDC, an ji labari cewa Babachir David Lawal ya dage wajen tallar Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso.
Tsohon jigon na APC ya zauna da ‘yan takaran jam’iyyar NDC domin ganin Najeriya ta je hannunsu a zaben da za a yi a badi.
Babachir ya ba Kwankwaso shawarwari ganin shi kwararren injiniyan ruwa ne daga Arewa ta yadda jama’a za su zabe su a 2027.
Asali: Legit.ng

