Shugaba Trump Ya ga Ta Kansa, an Yi Masa Ihu a wajen Wasan Kwallo

Shugaba Trump Ya ga Ta Kansa, an Yi Masa Ihu a wajen Wasan Kwallo

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kafa tarihi da ya halarci wasan karshe na gasar kwallon kwando a birnin New York
  • Trump ya halarci wurin ne tare da wasu manyan jami'ai a gwamnatinsa a wasan wanda aka gudanar a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026
  • Sai dai, kafin a fara wasan a filin Maddison Square Garden, wasu daga cikin mutanen da ke wajen sun yi wa shugaban kasar na Amurka ihu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin New York, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fuskanci gagarumar ihu na kushewa daga taron jama'a.

An yi wa Shugaba Trump ihun ne kafin a fara wasan ƙarshe na gasar kwallon kwando ta NBA a babban filin wasa na Madison Square Garden da ke birnin New York.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi maganar biyan Boko Haram kudin fansa kafin a ceto mutane 360

An yi wa Donald Trump ihu
Shugaba Donald Trump a wajen wasan karshe na NBA Hoto: Samuel Corum
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026, kafin a fara wasan.

An yi Trump ihu a bainar jama'a

Ihun kushewar ya ɓalle ne daga masoya ƙwallon kwando lokacin da aka nuna shugaban ƙasar na jam'iyyar Republican, wanda ke kallon wasan daga wani sashi na musamman na manyan baƙi a babban allon filin wasan a lokacin da ake rera taken ƙasa.

Sowa da rera muryoyin "USA! USA! USA!" sun ɓalle yayin da aka fara rera waƙar taken ƙasar kuma allon ya koma kan Trump.

Daga baya kuma ihu mai ƙarfi na kushewa ya ɓalle yayin da allon ya ci gaba da tsayawa a kan Trump, kamar yaddda bidiyon da CNN ta sanya ya nuna.

Shugaba Trump ya kafa tarihi

Shugaba Trump kafa tarihi a Madison Square Garden sakamakon halartwar wasan na karshe da ya yi, tashar Axios ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi gyara a tsarin Imprest, ta rage kudin da ake ba ministoci a Najeriya

Trump yana halartar wasa na uku na gasar ƙarshe ta NBA tsakanin ƙungiyar Knicks da Spurs, inda ya zama shugaban ƙasar Amurka mai ci na farko da ya taɓa halartar wasan ƙarshe na gasar NBA.

Ministan cikin gida, Doug Burgum; shugaban hukumar kare muhalli, Lee Zeldin; Ministan garkokin sufuri, Sean Duffy, Kai Trump da kuma Jared Kushner sun kasance tare da shugaban ƙasar yayin da ƙungiyar Knicks ke karɓar bakuncin wasansu na ƙarshe na farko a New York cikin shekaru da dama.

Trump ne shugaban ƙasa mai ci na farko da ya halarci wasan ƙarshe na NBA, kuma bayyanarsa ta jawo tsaurara matakan tsaro a kewaye da filin wasan da ke tsakiyar gundumar Manhattan.

Trump ya fuskanci ihu daga jama'a
Shugaba Donald Trump tare da mukarrabansa a wajen wasan karshe na NBA Hoto: Saul Loeb
Source: Getty Images

An tsaurara tsaro saboda ziyarar Trump

An rufe tituna a tsakiyar Manhattan, 'yan sanda sun kafa "yanki mai tsaro," sannan an soke taron kallon wasan da aka tsara gudanarwa a Madison Square Garden sakamakon ziyarar ta Trump.

Wani binciken ra'ayin jama'a da aka kammala ya nuna cewa amincewar jama'a ga salon mulkin Trump ta yi kasa sosai tun lokacin da ya fara siyasarsa.

Bayanan sun nuna cewa mafi yawancin 'yan Amurka suna sa ran farashin mai zai ci gaba da yin tashin gwauron zabi sakamakon yaƙin da yake yi da ƙasar Iran.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

Trump ya gargadi Iran, Israila

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya gargadi Iran da Israila kan ci gaba da bude wuta.

Shugaban na Amurka ya bukaci kasashen biyu masu gaba da juna da su gaggauta tsagaita wuta bayan sun yi nusayar hare-hare.

Hakazalika, Trump ya ce killace tashoshin jiragen ruwan sojojin Iran da Amurka ta yi zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniya ta ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng