Gwamnati Ta Gano yadda MTN da Kamfanoni 37 Ke Samar da Wuta ba Tare da Izini ba
- Hukumar LASERC ta bayyana cewa kamfanoni 38 ciki har da MTN da Flour Mills suna ci gaba da ayyukan samar da lantarki ba tare da izini ba
- Rahoto ya nuna cewa kamfanonin da abin ya shafa suna da karfin samar da kusan megawatt 600 na wutar lantarki a fadin jihar Legas
- LASERC ta ce kamfanonin sun kasa bin ddokokin jihar Legas kan gudanar da harkokin lantarki duk da ci gaba da tuntubarsu da hukumar ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Legas (LASERC) ta saki sunayen kamfanoni 38 da ke gudanar da ayyukan samar da lantarki ba tare da izini ba.
LASERC ta ce wadannan kamfanoni sun gaza sabunta lasisi ko daidaita takardunsu da hukumar duk da umarnin da aka ba su a lokuta daban daban.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta yi magana kan sace Janar da matarsa, ta fadi kokarin da take yi

Source: Twitter
Kamfanoni 38 sun ki sabunta lasisin wuta
Rahoton Punch ya nuna cewa daga cikin kamfanonin akwai MTN, Flour Mills, Golden Penny, First Global Commerce Solutions Limited, African Steel Mills Nigeria Limited da Lekki Port LFTZ Enterprise Limited.
An bayyana cewa wadannan kamfanoni gaba daya suna da karfin samar da kusan megawatt 600 na wutar lantarki.
LASERC ta ce kamfanonin suna rike da lasisai daban-daban da tsohuwar hukumar NERC ta bayar kafin jihar Legas ta kafa nata tsarin kula da lantarki.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa kamfanonin ba su fara bin tsarin neman sababbin lasisai da ake bukata a karkashin dokokin jihar Legas ba.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce:
“Har yanzu wadannan kamfanoni 38 ba su nemi lasisin da ya dace ko daidaita takardunsu da LASERC ba duk da sanarwa da gargadin da aka yi musu.”
Manyan kamfanoni da abin ya shafa
Daya daga cikin manyan kamfanonin da ke cikin jerin shi ne First Global Commerce Solutions Limited, wanda ke da lasisin samar da megawatt 77 na lantarki a Ebute-Meta.
Kamfanin Flour Mills Nigeria Plc ma yana cikin jerin tare da cibiyar samar da megawatt 74.5 a Apapa.
Haka kuma Lekki Port LFTZ Enterprise Limited yana da cibiyar samar da megawatt 30 a yankin Lekki Free Trade Zone.
Sunan kamfanin MTN Nigeria ya fito sau uku a cikin jerin saboda cibiyoyin samar da wuta daban-daban da yake da su a jihar Legas.
An bayyana cewa MTN na da cibiyoyi masu karfin megawatt 3.46 a Apapa, megawatt 4.5 a Ojota Switch Energy Centre 4 da kuma megawatt 5.4 a Ojota Switch Energy Centre 5.

Source: Original
Sauran kamfanonin da abin ya shafa
Shi ma kamfanin Golden Penny Power Limited ya fito sau uku a jerin tare da cibiyoyin samar da wuta masu karfin megawatt 32.4, 26 da kuma 57.2.
Wasu kamfanonin da LASERC ta ambata sun hada da African Steel Mills Nigeria Limited, CHI Limited, CCK Electric Power Technology Company Limited da Uraga Power Solutions Limited.
A4&T Power Solutions Limited na gudanar da ayyuka a wasu yankuna na Epe yayin da Solad Integrated Power Solutions Limited ke aiki a Balogun Modern Market da ke Legas.
An ba jihohi damar kula da wutar lantarki
Tun da fari, Legit ta ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta ba jihohi 36 na Najeriya damar su kafa kamfanonin samar da wutar lantarki da kula da rarrabata.
Rahoto ya ce dokar wutar lantarki ta 2023 da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rattaba hannu a kanta ta ba jihohi damar gudanar da harkokin samar da wuta da kansu.
Gwamnati ta ce ba za ta iya daukar nauyin dukkan kudin da ake bukata a bangaren lantarki ba saboda akwai sauran sassa masu bukatar kudi kamar ilimi, lafiya, tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

