An Sanya Sabon Lokacin Yanke Hukunci a Shari'ar Sojojin da Suka Yi Yunkurin Kifar da Tinubu

An Sanya Sabon Lokacin Yanke Hukunci a Shari'ar Sojojin da Suka Yi Yunkurin Kifar da Tinubu

  • Kotun sojoji ta sake ɗage yanke hukuncin shari’ar wasu jami’ai da ake zargi da hannu a wani yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu
  • An sauya ranar yanke hukuncin daga 30 ga Satumban 2026 wanda ya zama karo na huɗu da aka ɗage shi
  • Hukuncin zai tantance ko za a amince da wasu bayanan da ake zargin jami’an leƙen asiri sun karɓa daga waɗanda ake tuhuma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta sake ɗage yanke hukuncin Babbar Kotun Soji (GCM) da ke sauraron shari’ar wasu jami’an sojoji da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An shirya yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 30 ga Satumba 2026, amma yanzu an mayar da shi zuwa Litinin, 5 ga Oktoba 2026.

Za a yanke hukunci a shari'ar yunkurin juyin mulki
Babban hafsan hafsoshi, Janar Olufemi Oluyede Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

An sanya sabon lokaci

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tattara manoma kusan 50 zuwa daji, sun nemi makudan kudin fansa

A cikin sanarwar da aka aikewa mambobin kotun da sauran waɗanda lamarin ya shafa, sojojin sun ce zaman da aka ɗage zuwa ranar Laraba ba zai gudana ba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

“An ɗage zaman GCM da aka mayar zuwa Laraba, 30 ga Satumba 2026, zuwa Litinin, 5 ga Oktoba 2026,” in ji sanarwar.

An ce sabon zaman zai fara ne da ƙarfe 10:00 na safe a Scorpion Officers’ Mess, Asokoro, Abuja.

Sanarwar da Major M.U. Ardo, jami’in hulɗa da kotun, ya sanya wa hannu, ba ta bayyana dalilin ɗage zaman ba, sai dai ta nemi afuwar duk wata damuwa da hakan zai iya haifarwa.

Karo na huɗu kenan da aka ɗage hukuncin

Wannan shi ne karo na huɗu da aka ɗage yanke hukuncin, lamarin da ya ƙara tsawaita lokacin da ake jira domin samun matsaya kan shari’ar jami’an sojojin.

Ana sa ran hukuncin zai tantance ko za a amince da wasu bayanan da ake zargin an karɓa daga wasu daga cikin jami’an da ake tuhuma.

Batun ya biyo bayan wata shari'a cikin shari’a da kotun ta gudanar domin tantance yadda aka samu bayanan da kuma ko sun cika sharuddan da doka ta tanada kafin a amince da su a matsayin hujja.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke matasa saboda sanya rigar 'Tinubu Must Go'

Lauyoyin wadanda ake kara sun ƙalubalanci bayanan

Lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun ƙalubalanci shigar da bayanan cikin shari’ar, suna zargin cewa jami’an Hukumar Leken Asiri ta Tsaro (DIA) sun tilasta wa wasu daga cikin jami’an yin ko sake rubuta bayanan da suka ƙunshi abin da suke cewa ba gaskiya ba ne.

A yayin shari'ar cikin shari’ar, lauyoyin wadanda ake kara sun ce bayanan ba su cika wasu sharuddan doka da ake buƙata kafin a amince da su ba.

Sun kuma yi zargin cewa lauyoyi ko shaidu da wasu daga cikin jami’an da ake tuhuma suka zaɓa ba su halarta lokacin da aka ɗauki bayanan ba.

Za a yanke hukunci a shari'ar yunkurin juyin mulki
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta gabatar da shaidu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta shirya gabatar da shaidu 30 domin su bayar da shaida kan zargin juyin mulki.

Gwamnatin ta shirya gabatar da su ne a gaban kotu kan wasu mutane shida da ake zargi da kitsa yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng