Tirkashi: Sabuwar Rigima Ta Barke tsakanin Kwankwaso da Shugabannin NDC

Tirkashi: Sabuwar Rigima Ta Barke tsakanin Kwankwaso da Shugabannin NDC

  • Da alama za a kai ruwa rana tsakanin shugabannin jam'iyyar NDC reshen jihar Kano da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Shugabannin na NDC sun zargin Kwankwaso da kin mutunta yarjejeniyar da aka kulla kan tsarin iko da jam'iyyar
  • Sai dai, kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani kan zarge-zargen da aka jingida da dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wani sabon rikici ya ɓalle a cikin jam'iyyar NDC reshen jihar Kano biyo bayan zargin da shugabannin jam'iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma suka yi kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugabannin na NDC sun yi zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana ƙoƙarin ƙwace ragamar jam'iyyar tare da gurgunta mambobin da ba sa cikin tafiyar Kwankwasiyya.

Shugabannin NDC sun yi zargi kan Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron jam'iyyar NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce zargin yana ƙunshe ne a cikin wata takardar koke da mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Mohammed Serina, da shugaban jam'iyyar na jihar Kano, Hussaini Mariga suka fitar tare.

Kara karanta wannan

Babachir ya fadi gwamnonin da ke zawarcin ya koma APC bayan barin ADC

Shugabannin NDC na takun saka da Kwankwaso

Shugabannin sun bayyana cewa sun jawo hankalin jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson, a hukumance game da wannan lamari.

Jami'an na jam'iyyar sun yi iƙirarin cewa, ko da yake an karɓi Kwankwaso hannu bibbiyu a NDC kuma aka ba shi gagarumin tasiri a Kano, ana zargin sa da neman ikon mallakar tafiyar jam'iyyar baki ɗaya a kan mambobin da suka kafa ta da sauran masu ruwa da tsaki.

Serina ya bayyana cewa saɓani ya fara bayyana ne a lokacin tarurrukan gangamin jam'iyyar na jiha lokacin da ake zargin Kwankwaso ya yi yunƙurin karɓe ikon reshen jihar Kano baki ɗaya.

An yi zarge-zarge kan Kwankwaso

Jami'an sun yi zargin cewa duk da yarjejeniyar da aka yi, takaddama ta sake ɓallowa a lokacin tsarin bayar da takarar shugabanci lokacin da aka raba fom-fom na neman muƙaman zaɓe.

Serina ya yi iƙirarin cewa bayan mika fom-fom ɗin ga Kwankwaso, ana zargin sa da ƙin bayar da su ga mambobin jam'iyyar waɗanda ba mambobin tafiyar Kwankwasiyya ba.

Kara karanta wannan

Lokuta 6 da Atiku ya nemi samun kujerar shugaban kasa da yadda takarar ta kasance

Shugabannin jam'iyyar sun yi zargin cewa babu ko guda ɗaya daga cikin fom 40 na majalisar dokokin jiha, fom 24 na Majalisar wakilai, fom uku na Majalisar Dattawa ko fom na takarar gwamna da aka bai wa 'yan takara na wajen tafiyar Kwankwasiyya.

An zargi Kwankwaso da babbake komai

Mataimakin shugaban na ƙasa ya ƙara da iƙirarin cewa Kwankwaso ya ƙi ba da fom na takara ga shugaban jam'iyyar na jiha, mataimakin shugaban shiyya da sauran jami'an jam'iyyar waɗanda ba sa ƙarkashin tafiyar sa ta siyasa.

Sun kuma zargi tsohon gwamnan da barazanar barin jam'iyyar idan har ba a ba shi cikakken ikon ragamar ta a Kano ba.

Ana zargin Kwankwaso da babbake komai a NDC
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwasiyya ta yi martani

Da take mayar da martani kan zargin, kungiyar Kwankwasiyya ta yi watsi da shi, inda ta bayyana shi a matsayin mara tushe.

A wata hira ta musamman da jaridar The Punch, mai magana da yawun Kwankwasiyya, Habibu Muhammed, ya jaddada cewa babu wani ɗan takara da aka hana samun fom na takara.

Kwankwaso ya magantu kan jagorantar zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nesanta kansa da batun shirin jagorantar zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta cewa yana shirin jagorantar zanga-zanga domin nuna adawa da matsalar rashin tsaro.

Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana cewa baya goyon bayan abin da zai sanya a samu karyewar doka da oda a cikin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng