Trump Ya Fadi Dalilin Kin Yaki da Kim Jong Un duk da Yana da Nukiliya kamar Iran

Trump Ya Fadi Dalilin Kin Yaki da Kim Jong Un duk da Yana da Nukiliya kamar Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a matsayin abokinsa, yana mai cewa zai kasance cikin kwanciyar hankali
  • Trump ya kuma yi magana kan makaman nukiliyar Koriya ta Arewa, yana cewa ƙasar na da makaman nukiliya da yawa amma ba su kai na Amurka ba
  • Kalaman na zuwa ne yayin da Trump ke neman sake farfaɗo da tattaunawa da Kim Jong Un, duk da cewa Koriya ta Arewa ba ta tabbatar da hakan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a matsayin abokinsa, yayin da yake magana kan batun makaman nukiliyar Pyongyang.

Trump ya yi wannan furucin ne a Washington, DC, ranar Talata, bayan wani ɗan jarida ya tambaye shi dalilin da ya sa Koriya ta Arewa za ta iya mallakar makaman nukiliya yayin da Iran ba za ta iya ba.

Kara karanta wannan

2027: Rarara ya sake fitowa da maganganu masu zafi kan 'yan Arewa da Tinubu

Kim Jong Un da Donald Trump
Donald Trump a hagu da Kim Jong Un a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya ce Kim abokinsa ne

Al Jazeera ta wallafa cewa Trump ya ce Kim Jong Un abokinsa ne kuma shi ne kusan mutum ɗaya tilo a duniya da shugaban Koriya ta Arewar ke so.

A cewar Trump, Kim yana girmama shi kuma yana son shi, don haka ya ce:

“Muddin ina nan, zai kasance cikin kwanciyar hankali.”

Trump ya kuma ce ƙarfin makaman nukiliyar Koriya ta Arewa “yana da yawa”, amma ba ya kai na Amurka.

Adadin nukiliyar Koriya

Trump ya ce Koriya ta Arewa tana da makaman nukiliya 57, yayin da Ministan Tsaron Koriya ta Kudu, Ahn Gyu-back, ya bayyana a watan Agusta cewa ana kiyasta ƙasar na da tsakanin 80 zuwa 120.

Sai dai Ahn ya fayyace cewa wannan kiyasi ya samo asali ne daga binciken ƙungiyoyin bincike masu zaman kansu, kuma rundunar sojin Koriya ta Kudu ba ta iya tabbatar da takamaiman adadin ba.

Trump na son tattaunawa da Kim

Kara karanta wannan

Iran ta bankado karairayin Trump, ta yi masa barazana a yankin Gabas ta Tsakiya

Trump ya gana da Kim Jong Un a tarukan da aka gudanar a shekarar 2018 da 2019, amma tattaunawar ta tsaya bayan Amurka ta buƙaci Pyongyang ta yi watsi da makamanta na nukiliya.

Tun daga lokacin, Koriya ta Arewa ta ci gaba da bunƙasa shirinta na makamai masu linzami masu ɗaukar makaman nukiliya.

Kim Jong Un
Kim Jong Un a wajen wasu makamai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya kuma bayyana a baya cewa yana shirin tattaunawa kai tsaye da Kim kafin ƙarshen shekarar 2026, amma Koriya ta Arewa ba ta tabbatar da irin wannan ganawa a hukumance ba.

Ga bidiyon Trump da CBS ta wallafa a X:

Batun yaki da Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa Trump ya ce yaƙin da Amurka ke yi da Iran zai ƙare “nan ba da jimawa ba”, yayin da ya sake jaddada cewa Iran ba za ta samu makamin nukiliya ba.

Masu shiga tsakani daga Qatar sun ci gaba da ƙoƙarin sasanta Amurka da Iran kan shirin sake buɗe mashigar Hormuz da kuma dawo da tattaunawar nukiliyar ƙasar.

Sai dai har zuwa yanzu, bangarorin biyu sun ci gaba da samun saɓani kan sharudan yarjejeniyar, yayin da Araghchi ya ce Iran na jiran martanin Amurka kan shawararta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng