Babbar Magana: An Kai Harin da Ya Yi Barna Mai Girma a Tsakiyar Israila

Babbar Magana: An Kai Harin da Ya Yi Barna Mai Girma a Tsakiyar Israila

  • Jami'an lafiya na gaggawa sun kai dauki bayan da aka kai wani hari a tsakiya kasar Israila wanda ya jawo asarar rai
  • Harin ya kuma ya kuma jawo wasu mutane daban sun jikkata bayan da aka bude wuta daga cikin mota a wasu wurare
  • Ma'aikatar harkokin wajen Israila ta tabbatar da aukuwar harin, inda ra jajantawa mutanen da lamarin ya ritsa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv - Jami'an lafiya na gaggawa sun mayar da martani sakamakon wani harin harbe-harbe daga mota da aka gudanar a Israila.

An gudanar da harbe-harben ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Yunin 2026 a tsakanin Kochav Yair da Tzur Natan a tsakiyar ƙasar Isra'ila.

An raunata mutane a wani hari a Israila
Ma'aikatan lafiya a wurin da aka kai hari a Israila Hoto: @warfareanalysis
Source: Twitter

Jaridar New York Post ta ce hukumar agaji ta Magen David Adom (MDA) ta ce harin ya jawo mutuwar mutum ɗaya sannan wasu guda shida sun samu raunuka.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano

An kai hari a tsakiyar Israila

Mutanen da suka jikkata sun samu raunukan da suka huda jiki, ciki har da mutane biyu da suka raunata da tsanani da kuma mutum uku masu matsakaicin rauni.

Ma'aikatan lafiya na MDA da jami'an lafiya na gaggawa sun tabbatar da mutuwar wani mutum mai shekaru kusan 30 bayan samun raunukan harbin bindiga.

Kuma sun samar da magani yayin da suke kwashe waɗanda suka raunatan zuwa babban asibitin Meir Medical Center da ke Kfar Saba da kuma Asibitin Beilinson Hospital da ke Petach Tikvah.

An samu asarar rai da raunata mutane

Hukumar 'yan sanda ta Isra'ila ta ce an ruwaito aukuwar harbi a wani gidan mai da ke Kochav Yair, tare da raunata mutane biyu, kamar yaddda jami'an lafiya suka bayyana.

Ma'aikatan lafiya na MDA da jami'an lafiya na gaggawa sun ruwaito cewa mutumin mai shekaru kusan 30 ba ya nuna alamun rai kuma yana da raunukan da suka huda jiki, inda suka tabbatar da mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

Sun kuma samar da maganin lafiya tare da jigilar wani mutum mai shekaru kusan 40 zuwa Asibitin Meir Medical Center wanda ke cikin yanayi mai tsanani da rashin tabbas, tare da raunukan da suka huda jiki.

Mutum 1 ya rasu a harin da aka kai a Israila
Mutane tsaye a wani gidan mai da aka kai hari a Israila Hoto: @NationOfEldia
Source: Twitter

Ma'aikatar harkokin waje ta yi jimami

Ma'aikatar harkokin wajen Israila ta tabbatar da aukuwar harin a wani rubutu da ta yi a shafinta na X.

"An kashe ɗan ƙasar Isra'ila ɗaya sannan wasu guda biyar sun raunata a cikin wani harin ta'addanci na harbe-harbe a yankin Sharon."
"Ɗan ta'addan ya buɗe wuta ga fararen hula a wurare mabanbanta kafin a kashe shi, lamarin da ya canza ranar yau da kullum ta zama mummunan mafarki ga iyalai marasa laifi."
"Muna alhinin wanda abin ya shafa wanda ya rasa ransa, kuma muna yi wa dukkan waɗanda suka raunata fatan samun cikakkiyar lafiya cikin sauri."

Amurka na zargin Israila

A wani labarin kuma, kun ji cewa ma'aikatar tsaron Amurka ta fara zargin kasar Israila da yi wa jami'an gwamnati leken asiri.

Ma'aikatar Pentagon ta kasar Amurka ta dauki matakin ɗaga matakin tantance barazanar leƙen asiri daga Israel zuwa mafi girma.

Majiyoyi sun bayyana cewa hakan na da nasaba da zargin kan wasu ayyukan tattara bayanai daga Isra'ila kan jami'an gwamnatin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng