Amaechi Ya Hango Barazanar da ke Fuskantar 'Yan Adawa idan Tinubu Ya Zarce a 2027
- Rotimi Amaechi ya ce idan APC ta sake lashe zaɓen 2027, wasu daga cikin shugabannin ADC za su bar siyasa saboda rashin samun nasara
- Tsohon gwamnan Rivers ya bukaci mata su koma jihohi da mazabunsu domin tattara ƙuri’u, yana mai cewa hakan zai taimaka wa ADC
- Amaechi ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙara yawan talauci, tare da cewa yawancin ’yan Najeriya, musamman na Arewa, na fuskantar matsalolin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan zaben 2027.
Amaechi ya ce shugabannin jam’iyyar ADC da dama za su yi ritaya daga siyasa idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.

Source: Twitter
Amaechi, wanda tsohon gwamnan Jihar Rivers ne, ya bayyana hakan ne yayin taron ADC National Women League da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, 30 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Pantami na murnar samun tikitin PDP, abokin hamayyarsa ya sha alwashin jawo masa matsala
Amaechi ya bukaci mata su nemo ƙuri’u
Tsohon Ministan Sufuri ya yi kira ga matan ADC da su koma jihohinsu da ƙananan hukumominsu da mazabunsu domin gudanar da kamfen da kuma tattara ƙuri’u.
Ya kawo misalin zaɓen 2015, lokacin da APC ta kayar da PDP a matakin tarayya, yana mai cewa mata sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar APC a wancan lokaci.
“Mu shugabannin da kuke gani a nan, idan APC ta lashe zaɓen 2027, an yi mana ritaya daga siyasa. Don haka idan ba ku son mu yi ritaya daga siyasa, dole ne mu koma gida.”
Ya ƙara da cewa idan kowace mazaba ta ADC ta iya samar da ƙuri’u 2,000, jam’iyyar za ta iya samun nasarar zaɓen.
“Za ku gan ni a Kebbi, Yola, Rivers da Delta”
Amaechi ya ce ba za su ɗauki wani zaɓe da wasa ba, yana mai cewa zai shiga jihohi daban-daban domin yaƙin neman zaɓen ’yan takarar gwamna na ADC.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba
“Za ku gan ni a Kebbi, Yola, Rivers da Delta ina fafutukar zaɓen gwamna, domin ɗan takarar shugaban ƙasa ba zai iya mulki ba tare da gwamnoni ba,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga mata da su ƙarfafa mazajensu su fito su yi amfani da ƙuri’unsu.
Amaechi ya tuna da zaɓen 2015
Amaechi ya ce lokacin da APC ke ƙoƙarin kayar da gwamnatin PDP a 2015, jam’iyyar ta mayar da hankali sosai wajen amfani da tsarin ƙungiyoyin mata wajen wayar da kan masu zaɓe.
Ya ce a jihohin da suka je, mata suna kan gaba wajen gudanar da kamfen da kuma wayar da kan jama’a.
“Mun tabbatar mun gaya musu cewa idan ba su fito sun yi zaɓe ba, ba za mu yi nasara ba. Kuma suka fito. Mun yi yaƙin, muka yi nasara,” in ji shi.
Ya yi magana kan matsin tattalin arziki
Amaechi ya ce yanayin tattalin arzikin Najeriya yanzu ya fi tsanani fiye da lokacin zaɓen 2015, yana mai tambayar yadda ’yan Najeriya ke iya biyan kuɗin abinci da karatun ’ya’yansu.
Ya kuma yi ikirarin cewa yawan ’yan Najeriya da ke rayuwa cikin talauci da yara marasa zuwa makaranta ya ƙaru.
A cewarsa, lokacin da ya bar gwamnati a karkashin APC, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya kasance tsakanin miliyan 10 zuwa 12, amma ya yi ikirarin cewa yanzu adadin ya kai miliyan 20.
Amaechi ya yi kira ga mutanen Arewa
Amaechi ya kuma yi kira ga ’yan Arewa da su fito su yi amfani da ƙuri’unsu a zaɓen 2027. Ya ce idan mata a jihohin Arewa suka fito da yawa suka kada ƙuri’a, hakan zai iya sauya sakamakon zaɓe.
“Idan dukkan mata a Arewa suka fito suka yi zaɓe, Tinubu ba zai iya bayyana wani sakamako ba,” in ji Amaechi.

Source: Twitter
Wike ya ragargaji Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nyesom Wike, ya caccaki tsohon gwamnan Rivers kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC a 2027, Rotimi Amaechi.
Ministan na Abuja ya zargi Amaechi da yin watsi da jiharsu ta Rivers inda ya fifita wasu garuruwa fiye da na shi a gwamnatocin baya.
Asali: Legit.ng
