Ta Faru Ta Kare: Trump Ya Yi Maganar Kawo Karshen Yaki da Iran

Ta Faru Ta Kare: Trump Ya Yi Maganar Kawo Karshen Yaki da Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yi maganar karewar rikici da Iran bayan kalamansa da suka haifar da faduwar farashin man fetur
  • Trump ya ce Iran na fuskantar matsala sosai, yana kuma nanata cewa ƙasar ba za ta mallaki makamin nukiliya ba
  • Wani babban jami’in Iran, Ebrahim Azizi, ya ce Amurka da Isra’ila za su bar yankin daga ƙarshe, yayin da Iran da ƙasashen makwabta za su ci gaba da kasancewa a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Iran zai ƙare “nan ba da jimawa ba”.

Kalaman na Shugaba Donald Trump sun jawo faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Trump ya ce yaki da Iran ya zo karshe
Shugaba Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wani sabon tsarin gwamnatin tarayya da ke amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) a wani jawabi da ya yi a Washington, DC.

Kara karanta wannan

Iran ta bankado karairayin Trump, ta yi masa barazana a yankin Gabas ta Tsakiya

Trump ya ce Iran na fuskantar matsala

Trump ya ce Iran na “fuskantar matsala sosai”, tare da sake jaddada matsayinsa cewa ƙasar ba za ta mallaki makamin nukiliya ba.

“Wannan yaki zai ƙare nan ba da jimawa ba,” in ji Trump yayin da yake magana kan rikicin da Iran.

Ya ƙara da cewa Iran “ba za ta mallaki makamin nukiliya ba”, yana mai cewa farashin man fetur zai ci gaba da faɗuwa zuwa matakin da yake a baya.

Trump ya danganta yakin da abin da ya kira wata “ƙaramar tafiya” da ya yi zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kalaman shugaban na Amurka sun zo ne a daidai lokacin da kasuwannin duniya ke mayar da martani ga sababbin bayanai game da rikicin da kuma yiwuwar kawo ƙarshen tashin hankalin.

Wani babban jami’in Iran ya mayar da martani

A gefe guda, wani babban ɗan siyasar Iran, Ebrahim Azizi, ya ce daga ƙarshe za a tilasta wa Amurka da Isra’ila barin yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da Iran za ta ci gaba da kasancewa a yankin.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake kunyata Donald Trump

Azizi, wanda shi ne shugaban Kwamitin Tsaro na Ƙasa da Harkokin Wajen Majalisar Dokokin Iran, a wani rubutu a shafinsa na X, ya ce Amurka ba za ta ci gaba da kasancewa a yankin har abada ba.

“Ba makawa Amurka za ta bar wannan yanki, kuma kwanakin gwamnatin yahudawan [Isra’ila] sun kusa zuwa karshe,” in ji Azizi.

Ya ƙara da cewa daga ƙarshe Iran da ƙasashen da ke makwabtaka da ita ne za su ci gaba da kasancewa a yankin.

“Daga ƙarshe, mu da maƙwabtanmu ne za mu ci gaba da kasancewa a nan, muna fuskantar juna. Wannan ranar za ta kasance ranar nadama,” in ji shi.

Trump ya yi maganar yaki Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ba za ta tattauna da Amurka ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar ƙasar da ta halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) ba ta da wani shirin tattaunawa da Amurka.

A cewar Iran, ta gabatar da sharuɗɗa bakwai da za su taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng