Wata Sabuwa Ta Ɓullo, Ana Zargin Shugaba Tinubu na Kwance ba Shi da Lafiya a Kasar Waje
- Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na karkashin kulawar likitoci a Faransa
- Sowore ya ce wasu majiyoyi masu inganci sun sanar da shi cewa Tinubu na jinya a asibiti, amma bai san irin rashin lafiyar da ke damunsa ba
- Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta ce Tinubu na hutu ne a kasar Faransa kuma zai dawo Najeriya cikin makon nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na karbar magani a Faransa.
Wannan kalamai na fitaccen dan gwagwarmayar ya saba wa bayanin Fadar Shugaban Kasa, wadda ta ce Tinubu na cikin koshin lafiya, yana hutawa ne a Faransa.

Source: Facebook
Sowore ya yi wannan ikirarin ne yayin wata hira da shirin Prime Time na tashar Arise TV a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, 2026.
Dan takarar ya yi magana kan tsawaita zaman Tinubu a Turai da kuma rashin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 da aka gudanar a New York.
Sowore ya fadi halin da Tinubu ke ciki
Da aka tambaye shi hujjar da yake da ita kan ikirarinsa cewa a halin yanzu Tinubu na kwance a asibiti, Sowore ya ce bayanan sun fito ne daga majiyoyin da yake ganin abin dogaro ne.
Sai dai Sowore ya bayyana cewa bai san irin rashin lafiyar da ake zargin shugaban na fama da ita ba.
“Ba abin da aka fada min ba ne. Abin da na gano ne,” in ji Sowore.
Ya ce ya shafe makonni biyu da suka gabata a Amurka, inda yake bibiyar abubuwan da ke faruwa dangane da babban taron Majalisar Dinkin Duniya, sannan ya tuntubi wasu majiyoyi kan inda shugaban yake.

Kara karanta wannan
2027: Gwamna ya yi alƙawarin gyara Najeriya cikin shekaru 4 idan ya zama shugaban ƙasa
Wace rashin lafiya ke damun Tinubu?
“Akwai wani abu da ba na son bayyana wa a bainar jama’a,” in ji shi, inda ya kara da cewa “wasu daga cikin wadannan majiyoyi masu inganci sun ce Tinubu na jinya.”
Sai dai Sowore ya ce ba shi da cikakken bayani kan yanayin rashin lafiyar da ake zargin shugaban na fama da ita.
“Ban san irin rashin lafiyar ba saboda ba mu da wadannan bayanan, kuma shi ya sa ba a sallame shi daga asibiti ba,” in ji shi.
Ya kuma yi zargin cewa bayyanar Tinubu a bainar jama’a lokaci zuwa lokaci na da nufin samar da tunanin cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum.
Tinubu ya shafe lokaci a Turai
Wannan ikirari ya zo ne a daidai lokacin da ake kara mayar da hankali kan tsawaita zaman Tinubu a kasashen waje.
Shugaban ya bar Najeriya a ranar 30 ga Agusta domin abin da Fadar Shugaban Kasa ta fara bayyana a matsayin hutun shekara na tsawon makonni uku, inda ya fara tafiya zuwa Landan kafin daga bisani ya zarce Paris a Faransa.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An ɗauko batun da zai tsoratar da 'yan Arewa kan shirin dawo da tallafin fetur

Source: Twitter
Fadar Shugaban Kasa ta ci gaba da yin watsi da damuwar da ake nunawa game da lafiyar Tinubu, inda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce shugaban yana “cikin koshin lafiya” kuma zai dawo Najeriya cikin mako.
Sowore ya shiga zanga-zanga a Amurka
Kun ji cewa Omoyele Sowore ya shiga zanga-zangar neman kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da nuna goyon baya ga Falasɗinawa a New York da ke Amurka.
Sowore, wanda shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters, ya shafe shekaru da dama yana shiga zanga-zangar tituna da fafutukar siyasa a Najeriya.
Asali: Legit.ng
