Matar Sarki a Gombe Ta Rasu, Inuwa, Sheikh Pantami Sun Yi Ta'aziyya

Matar Sarki a Gombe Ta Rasu, Inuwa, Sheikh Pantami Sun Yi Ta'aziyya

  • Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jajanta wa Mai Kaltungo, Saleh Muhammad Umar, kan rasuwar matarsa, Hajiya Amina Saleh Muhammad
  • Hajiya Amina ta rasu ne ranar Laraba bayan gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jefa fadar Mai Kaltungo da al’ummar masarautar cikin jimami
  • Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, shi ma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Mai Kaltungo da iyalansa kan rasuwar Hajiya Amina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe – Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhini kan rasuwar Hajiya Amina Saleh Muhammad, matar Mai Kaltungo kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Gombe, Injiniya Saleh Muhammad Umar.

Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Amina ta rasu ne ranar Laraba bayan gajeruwar rashin lafiya.

Hajiya Amina Saleh Muhammad
Matar Sarkin Kaltungo da ta rasu. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Gwamna Inuwa ya yi ta’aziyya

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya rasu a Najeriya, majalisar tarayya ta karrama shi

A sakon da Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook, Inuwa Yahaya ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai mutunci, tausayi da sadaukarwa, wadda ta kasance mai ba mijinta da masarautar Kaltungo goyon baya.

Gwamnan ya ce rasuwarta babban rashi ne ba ga Mai Kaltungo da iyalansa kawai ba, har ma ga masarautar gargajiya da Jihar Gombe baki ɗaya.

A cewarsa, Hajiya Amina ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar fadar Mai Kaltungo, tare da bayar da gudunmawa wajen zaman lafiya.

Gwamna ya mata addu'a

A madadin gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar jihar, Inuwa Yahaya ya mika ta’aziyyarsa ga Mai Kaltungo, iyalan gidan sarauta, Majalisar Gargajiya ta Kaltungo da al’ummar masarautar.

Ya bukaci iyalan marigayiyar da su mayar da hankali wajen mata addu'a da tunawa da kyawawan halayenta da abubuwan alheri da ta bari a baya.

Gwamnan ya roki Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya saka mata da alherin da ta aikata, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdaus.

Pantami ya yi ta'aziyya

A nasa sakon ta’aziyya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana rasuwar Hajiya Amina a matsayin babban rashi ga Mai Kaltungo, iyalansa da al’ummar masarautar.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya kori hadimarsa 'yar Kannywood daga mukaminta

Pantami ya ce ya samu labarin rasuwar da matuƙar baƙin ciki, yana mai cewa wannan lokaci ne na mika wuya ga hukuncin Allah Madaukakin Sarki.

A sakon da ya wallafa a Facebook, ya mika ta’aziyyarsa ga Mai Kaltungo, iyalan gidan sarauta, ’yan uwa, abokai da daukacin al’ummar Kaltungo, tare da rokon Allah Ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Za a yi sallar jana'izarta ne da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Mai Kaltungo da ke ƙaramar hukumar Kaltungo a Jihar Gombe a ranar 1 ga Oktoba 2026.

An kashe mai shayi a Yola

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta fara bincike kan rasuwar wani mai sayar da shayi, Muhammad Auwal Idris, a wani wurin sayar da shayi da ke Nassarawa a Yola ta Arewa.

Rahotanni sun ce marigayin yana hidimar kwastomomi ne lokacin da wani mutum daga cikin wani rukuni ya sayi shayi na N50, amma rikici ya ɓarke bayan Idris ya nemi a biya kuɗin shayin.

Lamarin ya rikide zuwa faɗa, inda aka ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen sun lakada wa Idris duka sosai har ya rasu, yayin da ’yan sanda suka fara bincike domin gano cikakken abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng