Babachir Ya Fadi Gwamnonin da Ke Zawarcin Ya Koma APC bayan Barin ADC

Babachir Ya Fadi Gwamnonin da Ke Zawarcin Ya Koma APC bayan Barin ADC

  • A kwanakin baya ne dai tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya raba gari da jam'iyyar ADC mai adawa
  • Babachir Lawal ya bayyana cewa gwamnoni da jam'iyyun siyasa sun yi ta kiransa ta waya bayan ya bar jam'iyyar ADC
  • Ya bayyana cewa tuni was gwamnonin jam'iyyar APC suka fara zawarcinsa domin ganin ya dawo cikinta don ci gaba da siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya yi magana kan komawa jam'iyyar APC.

Babachir Lawal ya bayyana cewa aƙalla gwamnoni biyar da aka zaɓa a ƙarkashin jam'iyyar APC sun tuntuɓe shi biyo bayan murabus ɗinsa daga ADC.

Ana zawarcin Babachir Lawal don komawa APC
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Babachir David Lawal
Source: Twitter

Babachir Lawal ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar The Punch, kwanaki kaɗan bayan ficewarsa daga ADC sakamakon zargin cewa an tafka magudi a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon shugaban UNILORIN ya rasu bayan ya dawo daga sallar Isha'i

Gwamnonin APC na zawarcin Babachir

“Akwai kusan jam'iyyun siyasa biyar da suka kira ni a ranar Laraba, suna cewa za su danka mini jam'iyyunsu idan ina so. Idan kaji matsayin mutanen da suka kira ni domin yaba mini, ba za ka yarda ba."
"Yayin da muke magana dake, kusan gwamnonin APC biyar ko shida, waɗanda abokaina ne, sun tuntuɓe ni kuma suka tambaye ni, ‘Oga, yanzu za ka dawo gida?’
“Zan iya shaida maka da kwarin gwiwa cewa kusan gwamnoni masu ci biyar sun tuntuɓe ni, amma ba na tunanin dawowa a halin yanzu. Har ma da wasu ministoci sun so sanin ko zan duba yiwuwar dawowa APC. Na shaida musu a'a saboda matsalar da ta sa na bar APC tana nan har yanzu.”
“Babu amfanin dawowa idan babu abin da ya canza. Wane ci gaba na yi idan na koma domin fuskantar irin waɗancan matsalolin."

- Babachir Lawal

Shin Babachir zai koma wata jam'iyyar?

Kara karanta wannan

Tafiyar Atiku ta shiga matsala a Gombe, 'yan ADC sun koma APC da PDP

Sai dai, tsohon SGF ɗin ya ce ba ya cikin gaggawa na haɗewa da wani tafarkin siyasa na daban, inda ya jaddada cewa ya janye na ɗan lokaci daga harkokin siyasa kuma ya koma gonarsa, yana mai ƙarawa da cewa siyasa ba gado ba ce a iyalinsa.

“Na koma gonar ƙauyenmu a halin yanzu. Ban gane abin da kuke nufi ba da kuke tambaya ta game da makomar siyasa ta ta gaba. Shin an haife ni a matsayin ɗan siyasa ne? Shin dole ne na kasance cikin siyasa har abada?"
"Ba ni da wata alaƙa da kowane ɗayan waɗannan gurbatattun 'yan siyasar. Dukkanmu mun haɗu ne a Abuja kuma yanzu na bar musu Abujan.”
“Mahaifina ba ɗan siyasa ba ne. Ban gaji siyasa daga kowa ba. Na sami hanyar shiga siyasa kuma zan iya barinta a duk lokacin da na zaɓa."

- Babachir Lawal

Babachir ya ce zai iya barin siyasa
Babachir Lawal na magana da manema labarai Hoto: Babachir Dabid Lawal
Source: Facebook

Wanda Babachir zai zaba a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Babachir David Lawal ya yi kakkausar suka ga tsarin jam'iyyun APC, PDP, ADC da NDC.

Babachir David Lawal ya ce yana iya zaben matashin dan takarar shugaban kasa a 2027 kan sauran azzaluman jam'iyyu.

Tsohon SGF din ya ce yana iya yin la’akari da jefa kuri’a ga 'dan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a AAC, Omoyele Sowore, a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng