Gwamnatin Tinubu Ta Saki Kudi, Za Ta Biyan 'Yan Kwangila 1200 Hakkokinsu

Gwamnatin Tinubu Ta Saki Kudi, Za Ta Biyan 'Yan Kwangila 1200 Hakkokinsu

  • 'Yan kwangila na cikin gida za su murmusa yayin da gwamnatin tarayya ta amince a fara biyansu basussukan da suka biyo
  • Gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar kudi ta fara biyan basussukan da 'yan kwangila na cikin gida suka biyo ta
  • Ma'aikatar kudi ta bayyana cewa an amince a fara biyan kudaden ne ga 'yan kwangila fiye da 1,240 a sassa daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ma'aikatar kuɗi da tattalin arziki ta tarayya ta fara biyan hakkokin 'yan kwangila na cikin gida wadanda suka biyo gwamnati.

Ma'aikatar kudin ta bayyana cewa ta amince da biyan kuɗaɗe ga 'yan kwangila fiye da 1,240 a sassan ma'aikatun gwamnati, hukumomi, da rassan gudanarwa.

Gwamnatin Tinubu ta ba 'yan kwangila hakkokinsu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mary-Ann Duke, babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin sadarwa kuma sakatariyar yaɗa labarai ta Ministan kuɗi, ta fitar a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi maganar biyan Boko Haram kudin fansa kafin a ceto mutane 360

'Yan kwangila za su samu kudade

A cikin sanarwar ta bayyana cewa amincewar ta biyo bayan wani shirin tantancewa da daidaitawa domin tabbatar da basussukan da aka biyo.

Duke ta ce 'yan kwangilar da ke da tabbatattun bashin kuɗi na Naira miliyan 100 ko ƙasa da haka aka ba wa fifiko a rukunin biyan kuɗaɗe na baya-bayan nan da za a yi, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Ma'aikatar kuɗi ta tarayya ta amince a biyan kuɗaɗe ga 'yan kwangila fiye da 1,240, wanda ke samar da tallafin kuɗi na gaggawa ga kasuwanni a faɗin ƙasar tare da ƙarfafa sadaukarwar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuranta na kuɗi."

- Mary-Ann Duke

'Yan kasuwa za su samu sauki

Ma'aikatar ta ce biyan kuɗaɗen zai samar da sauƙi ga kasuwancin 'yan ƙasa da kuma ƙananan masana'antu da matsakaita, wanda zai ba su damar komawa wuraren ayyukan kwangila, biyan ma'aikata, da kuma biyan masu samar da kayayyaki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi gyara a tsarin Imprest, ta rage kudin da ake ba ministoci a Najeriya

“'Yan kwangilar da aka ba wa fifiko don biyan kuɗi a rukunin baya-bayan nan su ne waɗanda ke da tabbatattun bashin kuɗi a kewayen Naira miliyan 100 ko ƙasa da haka."

- Mary-Ann Duke.

Gwamnatin tarayya ta biya 'yan kwangila kudadensu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Nawa Gwamnatin tarayya ta amince a biya?

Ma'aikatar ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta amince a biya fiye da Naira biliyan 700 na tabbatattun basussukan da ake binta ga 'yan kwangilar cikin gida a cikin watannin baya-bayan nan.

Sanarwar ta bayyana cewa a cikin watan Mayu kaɗai, an amince a biya kusan Naira biliyan 436.6, wanda ke nuna gagarumin hanzari a ayyukan biyan kuɗi da nufin buɗe hanyoyin kuɗi da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki.

A watan Janairu, 'yan kwangilar cikin gida sun hana Doris Uzoka-Anite, tsohuwar karamar ministar kuɗi, shiga cikin ma'aikatar.

Wata shida bayan haka, Majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti domin tattaunawa da ma'aikatar kuɗi kan basussukan da ake bin ta na 'yan kwangila.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranaku biyu a matsayin hutun Babbar Sallah (Eid al-Adha) ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka yi wa 'yan Boko Haram dabara wajen ceto mutane 360 da aka sace a Borno

Gwamnatin ta bayyana ranakun Laraba 27 ga Mayu da Alhamis 28 ga Mayu, 2026, a matsayin ranakun hutun ga ma'aikata domin bikin sallar layya.

A cewar sanarwar da aka fitar, gwamnatin ta ba da hutun ne domin nuna girmamawar ta ga addini da al’adun miliyoyin Musulman Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng