Jirgin Kasa Dauke da Fasinjoji Ya Gamu da Hatsari a Hanyar Warri, Itakpe
- An samu aukuwar hatsarin jirgin kasa dauke da fasinjoji a kan hanyar Warri zuwa Itakpe a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2027
- Hatsarin ya jawo asarar wasu daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin bayan da ya goce daga kan layin dogon da yake tafiya a kansa
- Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa an tura jami'an ba da agajin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Delta - Wani jirgin kasa dauke da fasinjoji ya gamu da hatsari bayan ya goce daga kan layin dogo a kan hanyar Warri zuwa Itakpe.
Fasinjoji uku ne suka rasa rayukansu biyo bayan gocewar da wani jirgin ƙasa ya yi daga kan layinsa a kan hanyar jiragen ƙasa ta Warri zuwa Itakpe.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa hatsarin jirgin kasan ya auku ne a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno
Hukumar NRC ta yi bayani
Yayin da take tabbatar da aukuwar gocewar jirgin, hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa a halin yanzu sassan jami'an ba da agajin gaggawa da hukumomin da abin ya shafa suna wurin da lamarin ya faru suna duba yanayin da ake ciki tare da samar da taimakon da ya dace.
Shugaban hukumar NRC, Dr. Kayode Opeifa, ya fitar da sanarwar da ke tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin kasan a shafin X.
“Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) tana tabbatar da cewa wani lamari da ya shafi layin jiragen ƙasa na Warri–Itakpe ya auku a yau."
“A halin yanzu jami'an ba da agajin gaggawa da hukumomin da abin ya shafa suna wurin da lamarin ya faru suna duba yanayin tare da samar da taimakon da ya dace."
“Hukumar tana sanya ido sosai kan yadda abubuwa ke gudana, kuma za a fitar da cikakkiyar sanarwa da zaran an samu ƙarin bayanai."
- Dr. Kayode Opeifa

Source: Original
Karanta wasu labaran kan jirgin kasa
- "Ku yafe mani," An ji wanda ya 'jawo' hatsarin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja
- NSIB ta gano wasu bayanai kan hatsarin jirgin Kaduna, an ji halin da fasinjoji 6 ke ciki
- Bidiyon lokacin da jirgin kasa ya murkushe wata mota a Legas, mutane sun magantu
- NRC ta tsara zirga zirgar jiragen kasa na musamman a lokacin laramar Sallah a Najeriya
Hukumar NRC ta dakatar da zirga-zirga
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu aukuwar hatsarin jirgin kasa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja wanda ya sanya jama'a cikin firgici.
Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta dauki matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyar Abuja-Kaduna har zuwa wani lokaci, sakamakon hatsarin da ya faru.
Hakazalika, shugaban hukumar NRC, Dr. Kayode Opeifa, ya karyata jita-jitar cewa jiragen kasan ba su da inganci, ya kuma ce an fara mayar da kudin tikiti ga dukkan fasinjojin da abin ya shafa.
Asali: Legit.ng
