Tsohon Hadimin Buhari Ya Shawarci Kwankwaso Ya Fice daga Jam'iyyar NDC

Tsohon Hadimin Buhari Ya Shawarci Kwankwaso Ya Fice daga Jam'iyyar NDC

  • Tsohon hadimin marigayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ba da shawara ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Bashir Ahmad wanda 'dan asalin Kano ne, ya shawarci madugun na Kwankwasiyya da ya fice daga jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya
  • Tsohon hadimin na Buhari ya nuna cewa idan Kwankwaso yana ganin ba a yi masa adalci a NDC, ya fita ya nemi wata jam'iyyar daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Bashir Ahmad, tsohon hadimi ga marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shawarar barin jam'iyyar NDC.

Bashir Ahmad, ya yi kira ga Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar, da ya fice daga cikinta idan har yana jin ana nuna masa rashin adalci.

An shawarci Kwankwasonya fice daga NDC
Bashir Ahmad da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan, Bashir Ahmad
Source: Facebook

Bashir Ahmad ya bayar da wannan shawarar ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga NDC, an ji dalilin fusatar Madugu

Wace shawara aka ba Rabiu Kwankwaso?

Matashin ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan barazanar Kwankwaso kan canza wasu 'yan takara da ɓangaren Kwankwasiyya ya gabatar da farko ga jam'iyyar NDC a jihar Kano.

"Idan har Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi amanna da gaske cewa shugabancin NDC na ƙasa ya nuna masa rashin adalci, to mataki mafi dacewa da zai ɗauka shi ne ya bar jam'iyyar kuma ya nemi burinsa na siyasa a wani wurin daban."
“Maimakon ya ci gaba da zama a jam'iyyar da yake jin an takura masa ko kuma ana mayar da shi saniyar ware, ya kamata ya nemi wurin da ya dace da burinsa kuma zai ba shi damar yin takara a kan sharuɗɗansa."

- Bashir Ahmad

Bashir Ahmad ya fadi halin Kwankwaso

Tun da farko a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa Kwankwaso ba zai iya zama jam'iyyar da bai da iko a cikinta ba.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta barke tsakanin Kwankwaso da shugabannin jam'iyyar NDC

"Na shaida wa mutane da dama cewa Sanata Kwankwaso ba zai iya zama cikin kwanciyar hankali a kowace jam'iyyar siyasa ba matukar ba shi ne yake da cikakken iko ba, musamman a kan tsarin jam'iyya na jihar Kano."
"Wannan na ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa ya bar APC a shekarar 2018, duk da cewa a lokacin za a iya cewa babu wani dandamalin siyasa mafi kyau da zai iya amfani da shi wajen ciyar da burinsa gaba."
"Ga Kwankwaso, riƙe cikakken iko a kan ragamar jam'iyya a Kano ya kasance babban al'amari da ba ya wasa a kansa."

- Bashir Ahmad

Bashir Ahmad ya yi magana kan Kwankwaso
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi barazanar barin NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi barazanar barin jam'iyyar NDC mai adawa.

Kwankwaso ya yi barazanar ne bayan da jam'iyyar ta canza manyan 'yan takara na ɓangaren kungiyar Kwankwasiyya a Kano.

An gudanar da canje-canjen ne domin tabbatar da yarjejeniyar da aka yi tun da farko a kan rarraba muƙaman jam'iyya da tikitin takarar zaɓe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng