Bola Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Ministoci 2 a Fadar Shugaban Kasa

Bola Tinubu Ya Rantsar da Sababbin Ministoci 2 a Fadar Shugaban Kasa

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci biyu a Fadar Shugaban Kasa da ke birnin tarayya Abuja a farkon makon nan
  • Joseph Olasunkanmi Tegbe ya zama sabon Ministan Wutar Lantarki bayan tantancewar da Majalisar dattawan Najeriya ta masa
  • Ambasada Sola Enikanolaiye, wanda ya fito daga Igbagun a jihar Kogi ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin Karamin Ministan Harkokin Waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci biyu a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, 2026 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Hakan ya biyo bayan tantancewa da amincewa da nadin sababbin ministocin da Majalisar dattawan Najeriya ta yi a makonnin da suka shige.

Shugaba Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana magana a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Bola Tinubu ya rantsar da ministoci 2

Daily Trust ta rahoto cewa waɗanda aka rantsar sun haɗa da Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin Ministan Wutar Lantarki, da Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin Karamin Ministan Ƙaramin Harkokin Waje.

Kara karanta wannan

2027: Ndume ya gargadi Tinubu da APC, ya ce suna da babban kalubale

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da bikin rantsarwar ne a gaban matan sababbin ministocin da kuma manyan jami’an gwamnati.

Dalilin nada sababbin ministoci 2

Tun farko dai Shugaba Bola Tinubu ya nada ministocin ne biyo bayan murabus ɗin tsofaffin ministoci biyu, wadanda suka ajiye aiki domin neman kujerar siyasa.

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar da kuma tsohon Ministan Wutar Lantarki Adebayo Adelabu sun yi murabus domin tsayawa takarar gwamna a jihohinsu.

Bayan hakan ne Shugaba Tinubu ya mika sunayen sababbin ministocin ga Majalisar Dattawa, inda aka tantance su tare da tabbatar da su a ranar 6 ga Mayu, 2026.

Takaitaccen tarihin Joseph Tegbe

Joseph Olasunkanmi Tegbe ɗan asalin birnin Ibadan ne da ke Jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya, yankin da shugaban kasa ya fito.

Sabon ministan kwararre ne a fannin gyare-gyaren tattalin arziki da tsarin gwamnati, inda ya shafe fiye da shekaru 35 yana aiki a bangarorin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

An san shi da kwarewa wajen tsara manufofi da kuma hulɗa da masu ruwa da tsaki, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan

Ndume: Sanata ya faɗi wurin da ya dace Amurka ta kafa sansanin soji a jihar Borno

Tegbe.
Sabon ministan harkokin lantarki na Najeriya, Joseph Olasunkanmi Tegbe Hoto: @aonanuga1956
Source: Instagram

Tarihin Ambasada Enikanolaiye

Ambasada Sola Enikanolaiye, wanda ya fito daga Igbagun a Jihar Kogi, ya samu digiri na farko mai daraja ta farko a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya kuma lashe lambar yabo ta mafi ƙwazo dalibi a tsangayarsa. Daga baya ya yi digiri na biyu a fannin Dokar Ƙasa da Hulɗar Ƙasa daga Jami’ar Legas.

A matsayinsa na jami’in diflomasiyya, ya yi aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashe da dama ciki har da Habasha, Sabiya, Kanada da Birtaniya.

A aikinsa na ƙarshe kafin wannan mukami, ya kasance Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Waje da Dangantakar Ƙasa da Kasa.

Tinubu ya ba Zainab Marwa mukami

Kun ji cewa Bola Tinubu ya zabi Dr. Zainab Marwa domin zama mamba a majalisar gudanarwa ta hukumar kula da ci gaban yankin Niger Delta (NDDC).

Tinubu ya miƙa sunan Dr. Zainab Marwa ga Majalisar dattawa domin tabbatar da ita a matsayin mamba a majalisar gudanarwa ta NDDC, mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.

An yi nadin ne da nufin cike gurbin da aka samu sakamakon murabus ɗin tsohon mamban hukumar da ya gabata, Hon. Abdulrazak Namdas

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262