2027: Shettima, Sanata Yari, Ganduje Sun Zauna da Rarara da Wasu 'Yan Fim

2027: Shettima, Sanata Yari, Ganduje Sun Zauna da Rarara da Wasu 'Yan Fim

  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci masu sana’o’in nishaɗi da fasaha a Arewa su marawa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen 2027
  • Shettima ya ce goyon bayan Tinubu ya zama wajibi domin tabbatar da ci gaban Najeriya da haɗin kan ƙasa, tare da alkawarin ci gaba da tallafa wa 'yan fim
  • Ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope ta kuma bayyana aniyarta ta goyon bayan Tinubu da sauran ƴan takarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci ƙwararrun masu sana’o’in nishaɗi da fasaha da ke Arewa su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen 2027.

Shettima ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin da ya karɓi wata tawaga ta masu fasahar nishaɗi daga Arewa ƙarƙashin ƙungiyar Triple-R a ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027

Rarara da yan fim tare da Kashim Shettima da Abdulaziz Yari
Mawakan Kannywood tare da wasu shugabannin Najeriya. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Shettima ya ce a zabi Tinubu

Mataimakin shugaban ƙasan ya wallafa a Facebook cewa Tinubu ya cancanci samun goyon bayan Arewa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da adalci da haɗin kan Najeriya.

Ya kuma tabbatar wa masu fasahar nishaɗin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su tallafa wa masu fasaha, ’yan fim da mawaƙa a yankin Arewa.

A cewarsa, yankin Arewa na da damar cin gajiyar shirye-shiryen gwamnatin Tinubu da suka shafi bunƙasa tattalin arzikin fasaha, adana al’adu da samar da guraben samun kuɗi.

Maganar Abdulaziz Yari

Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce sake zaɓen Tinubu a 2027 ya kamata ya kasance bisa la’akari da abubuwan da gwamnatinsa ta cimma.

Yari ya buƙaci ƙungiyoyin goyon baya da daidaikun mutane su duba ayyukan gwamnatin kafin yanke matsaya kan zaɓen.

Kara karanta wannan

Matsin da ake ciki yana damun Tinubu, ya fadi hanyar tsame mutane miliyan 5 daga talauci

Ya kuma yi watsi da ikirarin masu hamayya da gwamnatin cewa an ware Arewa wajen rabon muƙamai da ayyukan raya ƙasa, yana mai cewa yankin ya samu kulawa daga gwamnatin Tinubu.

Masari da Ganduje sun magantu

Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya gode wa masu sana’ar nishaɗin kan goyon bayan da suka yi alkawarin bai wa Tinubu da sauran ’yan takarar APC.

Yan fim a taron Abuja
Musa Mai Sana'a a wajen taro da jami'an gwamnati. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba wa ƙungiyar Triple-R, yana mai kira da a ƙara samar da kayayyakin more rayuwa da horar da sababbin masu fasaha a Arewa.

Ganduje ya ce ƙungiyar ta kasance ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke tallafa wa APC, tare da jaddada muhimmancin adalci da haɗin kai.

Dauda Kahutu Rarara, ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta marawa Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen 2027, tare da sauran ’yan takarar APC a Arewa.

Rarara ya yabawa Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa ya ba da gudummawa wajen samun nasarar jam’iyyar APC da kafa gwamnati.

Rarara ya kuma yi magana kan kalamansa na cewa dukkanin ’yan Kannywood da ke cikin ƙungiyarsu dole ne su zaɓi Tinubu a 2027.

Ya ce masu sukar Tinubu da dama ba su da ɗan takarar da suke goyon baya, saboda haka shi da ƙungiyarsa za su ci gaba da tallata Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng