Manyan Labarai A Yau
Akalla mutum 10 sun jikkata bayan rikici ya barke tsakanin al’ummomin Chirif Magaji da Chirif Dikko a karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto kan rikicin gona.
'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kashe jami'in tsaro tare da sace wani adadi mai yawa na mutane.
Sarkin Gazargamu, Mai Martaba Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti da ke kasar Masar bayn shafe tsawon lokaci yana jinya.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan yakin kasarsa da Iran. Trump ya bayyana cewa Amurka za ta samu cikakkiyar nasara kan kasar Iran.
Sabon ministan wutar lantarki, Joseph Tegbe ya bayyana cewa matsalolin karancin wutar Najeriya suna da yawa, ba zai yiwu a magance su cikin dan lokaci ba.
An samu rahoton hallaka wani mawaki dan asalin Najeriya a kasar Burtaniya. Mark Yinka Orabiyi wanda aka fi sani da Talay Riley, ya mutu ne bayan caka masa wuka.
Kungiyar NLC ta tabbatar da rasuwar shugaban JNC na jihar Legas, Domingo Michael Adaeleke a taron kwadago na duniya da ke gudana a birnin Geneva.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, na tattaunawa domin komawa jam'iyyar ADC. Nasiru Gawuna na son samun tikitin takara.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya halarci wasan karshe na gasar NBA. Sai dai, an yi wa shugaban kasar ihu a wajen wasan da aka yi a New York.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari