Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Soke Zaben Fitar da Gwani na Jam'iyyar APC a Jihar Gombe

Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Soke Zaben Fitar da Gwani na Jam'iyyar APC a Jihar Gombe

  • Babbar Kotun Tarayya da ke zama Gombe ta soke zaben fitar da gwanin APC na takarar Majalisar wakilai a mazabar Balanga/Billiri
  • Kotun ta hana Hon. Ali Isa J.C. sake tsayawa takara tare da umartar APC ta gudanar da sabon zaben fitar da gwani a mazabar
  • Kotun ta ce rashin saka sunan Ali J.C. cikin kundin rajistar mambobin APC da aka miƙa wa INEC ya sa takararsa ta saba da doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria- Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Gombe ta soke zaben fitar da gwanin APC da ya samar da Ali Isa J.C a matsayin dan takarar Majalisar wakilai na Balanga da Billiri.

A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Vera E. Ibrahim ta umarci APC ta gudanar da sabon zabe a wannan mazaba tare da hana Ali J.C. sake tsayawa takara.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya dawo daga kasar waje, ya fadi abin da za su yi wa Nyesom Wike

Kotu.
Gudumar da ake amfani da ita a zaman shari'a a kotunan Najeriya Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Kotu ta soke tikitin Hon. Ali Isa J.C

A rahoton Daily Trust, kotun ta kuma hana tsohon mai tsawatarwa na marasa rinjaye a Majalisar wakilai shiga sabon zaben da za a shirya nan gaba saboda ya karya doka.

Ta bayyana cewa takarar Ali J.C. a zaben fitar fa gwani na APC bai inganta ba, ya saba da doka, saboda rashin bin tanadin Sashe na 77 na Dokar Zabe ta 2026.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da wani ɗan takara, Hon. John Alfred, ya shigar, inda ya ƙalubalanci ingancin zaben fitar da gwani na APC da kuma fitowar Ali Isa J.C. a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a mazabar.

Kotun ta ce ba a saka sunan Ali J.C. cikin kundin rajistar mambobin APC da aka miƙa wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) aƙalla kwanaki 21 kafin zaben fitar da gwani ba, kamar yadda Sashe na 77 na Dokar Zabe ya tanada.

Kara karanta wannan

PDP ta sanar da sakamakon zaben fitar da gwani a Gombe, Pantami ya san makomarsa

Dalilin soke tikitin dan takarar APC

Mai ƙara, Mista John Alfred, ya shaida wa kotun cewa Ali J.C. ya shiga jam’iyyar ne kwanaki 16 kacal kafin zaben fidda gwani.

Mai Shari’a Ibrahim ta ƙara da cewa an gudanar da zaben ba tare da cikakken bin ƙa’idojin da doka ta tanada ba, lamarin da ya sa tsarin bai inganta ba.

Saboda haka, kotun ta soke takarar Hon. Ali Isa J.C. tare da umartar a janye takardar shaidar zama dan takarar APC a mazabar Balanga da Billiri.

Ali Isa J.C.
Dan takarar APC na Majalisar tarayya a Balanda/Billiri, sanda kotu ta soke, Ali Isa J.C. Hoto: Ibrahim Daudus
Source: Facebook

Kotun ta kuma umarci APC da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 30 domin zaɓar ɗan takararta a mazabar dan Majalisar tarayya.

Kotun ta dogara da sababbin hukunce-hukuncen Kotun Koli wajen bambance tsakanin takaddamar zama ɗan jam’iyya kawai da kuma bin ƙa’idojin doka da suka shafi kundin rajistar mambobin jam’iyya.

Pantami ya lashe zaben fitar da gwani

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya zama ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan Gombe na 2027.

Pantami ya zama halastaccen dan takarar PDP ne bayan kammala tattara sakamakon zaben fitar da gwani daga ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262