"Sun Samu Shahada": Jirgin Sama Dauke da Mutane Ya Gamu da Hatsari a Pakistan
- An samu aukuwar hatsari na wani jirgin helikofta na rundunar sojojin Pakistan a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026
- Jirgin saman ya fado ne jim kadan bayan tashinsa a yankin Kashmir, inda hukumomi suka ce matsalar inji ce ta jawo hatsarin
- Mahukunta sun bayyana cewa dukkanin mutanen da ke cikin jirgin saman a lokacin da ya tashi sun samu shahada bayan fadowarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Pakistan - Wani jirgin helikofta na rundunar sojojin Pakistan ya faɗi kusa da birnin Muzaffarabad da ke yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi.
Jirgin ya gamu da hatsari ne sakamakon matsalar inji, kamar yaddda dakarun sojan ƙasar suka bayyana, inda suka ƙara da cewa babu wanda ya tsira da ransa.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa rundunar sojojin kasar Pakistan ta sanar da fadowar jirgin a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026.
Mutane sun rasu a hatsarin jirgin sama
“Wani jirgin helikofta ƙirar Mi-17 na sashen dakarun sama na rundunar sojojin Pakistan ya faɗi kusa da Muzaffarabad a yau a lokacin da yake shirin tashi sakamakon matsalar inji."
“Dukkan ma'aikatan da ke cikinsa sun samu shahada."
Sai dai, sanarwar ba ta bayyana takamaiman adadin mutanen da suka mutu ba, sakamakon hatsarin da jirgin ya yi.
An jibge jami'an tsaro a yankin
An fuskanci gagarumar kasancewar jami'an tsaro a cikin kwanakin nan a Muzaffarabad bayan mambobin wata ƙungiya suka bayyana cewa za su gudanar da zanga-zanga jim kaɗan bayan da gwamnatin yankin ta dakatar da ƙungiyar a ƙarkashin dokokin yaƙi da ta'addanci.
Aƙalla mutane 11 ne aka kashe a ranar Lahadi, 7 ga watan Yunin 2026 a lokacin arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a birnin Rawalakot, babban birnin gundumar Poonch da ke yankin.
Tun daga lokacin, hukumomi a yankin Kashmir da Pakistan sun tura dakarun tsaro na tarayya, tare da bayar da tsauraran gargaɗin tafiye-tafiye ga yankin.
Yankin Kashmir wanda mafi yawancin mazaunansa Musulmi ne, ƙasashen Indiya da Pakistan baki ɗayansu suna iƙirarin mallakarsa, amma an raba shi a tsakaninsu tun bayan samun 'yancin kansu daga mulkin mallakar Biritaniya.

Source: Getty Images
Shugabannin Pakistan sun yi ta'aziyya
Tashar Euronews ta ce shugaban ƙasar Pakistan, Asif Ali Zardari, da FiraMinista Shehbaz Sharif sun bayyana alhininsu game da hatsarin jirgin, inda suka jinjina wa waɗanda suka rasa rayukansu..
Babban Kwamandan Askarawan Pakistan, Field Marshal Asim Munir, shi ma ya bayyana tsananin alhininsa game da rashin rayukan da aka yi sannan ya mika saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu.
Jirgin sama ya yi hatsari a Sudan ta Kudu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani karamin jirgin fasinja ya yi hatsari a ƙasar Sudan ta Kudu inda ya yi sanadin mutuwar dukkan mutane 14 da ke cikinsa.
An tabbatar da cewa jirgin ya faɗi ne da nisan kilomita 20 daga kudu maso yammacin babban birnin ƙasar, wato Juba da safe.
bayanan farko da aka samu sun nuna cewa hatsarin jirgin saman kirar Cessna 208 Caravan ya faru ne sakamakon rashin kyawun yanayi.
Asali: Legit.ng

